Dalilin da ya sa na amince a sayar da kadarar Najeriya ga kamfanin da ake tuhuma da laifin zamba - Malami

Dalilin da ya sa na amince a sayar da kadarar Najeriya ga kamfanin da ake tuhuma da laifin zamba - Malami

Lauyan koli kuma ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami, ya ce amincewar da ya bayar ta sayar da gangunan man fetur da aka kwato ga masu harkar mai ba ya cin karo da shari'a.

Ministan ya fito ya yi magana ne bayan ta bayyana cewa, ya ba da izinin a cefanar da wata haja ta danyen man fetur ga wani kamfani mai suna 'Omoh-Jay' duk da ana tuhumar kamfanin da laifin zamba.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, Malami ya bayar da umarnin sayar da wasu manyan gangunan danyen man fetur ga kamfanin bayan an karbe daga hannun barayin da ke fasa bututun kamfanin man fetur na kasa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, an tuhumar kamfanin da zargin barnatar da ton dubu 12 na danyen man fetur a shekarar 2009.

Da ya ke kare kansa, Malami ya ce izinin da bayar domin a yi gwanjon danyen man gwamnati ba laifi bane domin kuwa doka ta ba da damar hakan ta tabbata.

Ministan Shari'a; Abubakar Malami
Hoto Daga Businessday.ng
Ministan Shari'a; Abubakar Malami Hoto Daga Businessday.ng
Asali: UGC

A cewarsa, sashe na 36 cikin kundin tsarin mulkin kasa, ya bawa kamfanin Omoh -Jay damar shiga ciniki ko dillancin man fetur a Najeriya.

Ya ce kamfanin ya na da rijista da gwamnati kuma har yanzu kotu ba ta tabbatar da zargin laifin da ake tuhumarsa da aikata wa ba.

Malami ya ce, "Duk mutumin da ake tuhuma da aikata wani laifi za a dauki shi mara laifi har sai an tabbatar da shi mai laifi."

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Umar Gwandu ya fitar, Malami ya ce ofishinsa ya samu lamunin cefanar da danyen man biyo bayan umarnin da fadar shugaban kasa ta bayar a ranar 25 ga watan Oktoban 2018.

Ya ce an yi gwanjon danyen man ne a bisa tafarki na daidai kamar yadda wasu bayanai da ma'aikatar ayyuka, lantarki da gidaje ta fitar a kan darajar wannan kadarori.

A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, Majalisar dattawa a ranar Talata, 14 ga watan Yuli ta samar da sabuwar dokar daurin rai-da-rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a Najeriya.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Gwamnatin Tarayya ta shirya biyan bashin albashin malamai na makarantu masu zaman kansu

Majalisar ta yanke shawarar sauya dokar ne daga daurin shekaru 10 a gida gyara hali zuwa daurin rai-da-rai.

Dokar wadda Sanata Oluremi Tinubu, ta shigar na da take "Bukatar canza dokar laifi CAP. C.38 na dokokin tarayyar Najeriya 2004."

Hakazalika, dokar ta sauya tsarin cewa wajibi duk macen da aka yiwa fyade ta kai kara cikin wani takaitaccen lokaci na watanni biyu, ko kuma a karyata ta.

Bayan haka, an sauya tsarin cewa mata kadai ake yiwa fyade, yanzu dokar ta hada da maza.

A yanzu, komin dadewa da yiwa mutum fyade, zai iya shigar da kara kuma a saurara.

Yanzu za'a tura dokar majalisar wakilai domin su amince da ita kafin mika wa shugaban kasa ya rattaba hannu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel