Coronavirus: Gwamnatin Tarayya ta shirya biyan bashin albashin malamai na makarantu masu zaman kansu

Coronavirus: Gwamnatin Tarayya ta shirya biyan bashin albashin malamai na makarantu masu zaman kansu

- Gwamnatin tarayya ta amince da biyan bashin albashin malaman makarantu masu zaman kansu

- Shugaban kungiyar makarantu masu zaman kansu na kasa, Yomi Otubela, shi ne ya sanar da hakan

- A cewar Otubela, sanannun makarantun da suka kasance mambobin kungiyar su kadai ne za su ci moriyar wannan lamari

Gwamnatin Najeriya ta sanya farin ciki a zukatan malaman makarantu masu zaman kansu wadanda suka shiga cikin halin kakanikayi sanadiyar annobar korona.

Babu shakka biyan albashin malamai a makarantu masu zaman kansu ya tsaya tun bayan rufe kafatanin makarantu a fadin tarayya da aka yi saboda annobar korona.

Wani rahoto da jaridar Guardian ta ruwaito ya bayyana cewa, ana kyautata zaton gwamnatin tarayya za ta dauki nauyin biyan basussukan albashin malaman tun daga na watan Maris lokacin da aka shimfida dokar kulle.

Shugaba Muhammadu Buhari
Hakkin mallakar hoto: Fadar Shugaban kasa
Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: UGC

Cif Yomi Otubela, shugaban kungiyar masu mallakar makarantu masu zaman kansu ta NAPPS, shi ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai da suka yi da shi ta hanyar bidiyo.

A cewar Otubele, za a yi biyan bashin albashin malaman makarantun masu zaman kansu daga cikin naira tiriliyan 2.3 da gwamnatin tarayya ta ware na saukaka radadin annobar korona.

Ya bayyana cewa, kungiyarsu ce ta shigar da wannan bukata cikin wata wasika da ta aikewa majalisar tattalin arziki wadda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta.

KARANTA KUMA: WAEC 2020: Gwamnatin Tarayya ba ta da hurumin yanke hukunci a kan makarantu masu zaman kansu na gwamnatocin jihohi - Ministan Ilimi

Ya ce NAPPS ta shigar da bukatar neman gwamnatin tarayya ta tallafawa makarantu masu zaman kansu domin rage musu radadin kunci da annobar korona ta jefa su ciki.

A wani rahoto da gidan Talabijin na AIT ya ruwaito, Cif Otubele ya yi bayanin cewa, makarantun da suka kasance mambobin kungiyar ne kadai za su sharbi romon wannan tallafi da gwamnatin ta bayar.

Otubele cikin sanarwar ya kara da cewa, majalisar zartarwa wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta ta amince da wannan kudiri, inda suke yi wa gwamnatin godiya kan hanzarin karbar bukatar da tayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel