Yarinya mai shekaru 14 ta kashe kanta bayan kwaso cikin shege

Yarinya mai shekaru 14 ta kashe kanta bayan kwaso cikin shege

- Anita Haledu Ibrahim mai shekaru 14 ta kashe kanta bayan ta kwaso cikin shege yayin dokar kullen korona

- Anita daliba ce a makarantar gwamnati ta kimiyya da ke Andaha kusa da Akwanga a jihar Nasarawa

- Bayan samun cikin, saurayin ya amince da cewa nashi ne kuma zai aureta amma sai mahaifinta ya yi mata mugun duka

Yarinya mai shekaru 14 mai suna Anita Haledu Ibrahim ta kashe kanta bayan cikin shege da ta dauko.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Anita daliba ce a makarantar gwamnati ta kimiyya da ke Andaha kusa da Akwanga. Ta sha maganin kwari don kashe kanta a ranar Asabar, 11 ga watan Yulin 2020.

Kamar yadda majiyoyi suka sanar, saurayin Anita ya dirka mata ciki bayan haduwarsu a Andaha yayin kullen korona.

Sun shaku har ta samu ciki amma daga baya sai ta koma kauyensu da ke Abuja. Bayan iyayenta sun tuntubeshi, ya amsa cikin kuma ya bayyana bukatar aurenta.

Anita ta yanke hukuncin kashe kanta bayan mahaifinta, Haledu Ibrahim, ya yi mata mugun duka a kan cikin.

Ta sha maganin kwarin a ranar Asabar, 11 ga watan Yuli ammaan gaggauta kai ta asibiti inda ta cika a ranar 14 ga watan Yuli.

'Yan uwanta ma shirye-shiryen birneta.

Yarinya mai shekaru 14 ta kashe kanta bayan kwaso cikin shege
Yarinya mai shekaru 14 ta kashe kanta bayan kwaso cikin shege. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rahoton siya wa da gidan N300m: Malami ya yi barazanar maka wata jarida a kotu

A wani labari na daban, wani mutum mai shekaru 48 mai suna Umaru Aliyu ya shiga hannun jami'an tsaro saboda lalata yarinya mai shekaru 3 da yayi.

Wanda ake zargin ya yi wa yarinyar fyade ne a wani tafki da ke kusa da gidansa a yankin Mararaba ta karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Al'amarin ya faru a ranar 26 ga watan Mayun 2020 a sabuwar kasuwar lemu da ke karamar hukumar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Bola Longe, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin a wata tattaunawa da yayi da Punch a Lafia. Ya ce tuni aka kama wanda ake zargin.

Ya ce, "A ranar 27 ga watan Mayun 2020, an kai korafin wani Umaru Aliyu da ke sabuwar kasuwar 'yan lemu da ke karamar hukumar Karu. Ana zarginsa da lalata yarinya mai shekaru 3."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel