Da duminsa: Kotun koli ta kori karar Lagos da Ekiti na haramta zaman kotu a yanar gizo

Da duminsa: Kotun koli ta kori karar Lagos da Ekiti na haramta zaman kotu a yanar gizo

- Kotun koli ta kori karar da jihohin Lagos da Ekiti suka shigar na haramta zaman kotu a yanar gizo

- Mai shari'a Olabode Rhodes-Vivour ya ce babu laifi a zaman kotu a yanar gizo

- Kotun kolin ta yi barazanar hukunta duk wani mai shari'a da yaki gudanar da zaman kotunsa ta yanar gizo

Rahotannin da ke shigowa a yanzu na nuni da cewa kotun koli ta yi watsi da karar da jihohin Lagos da Ekiti suka shigar, inda suke kalubalantar halascin gudanar da zaman kotu a yanar gizo.

A wani hukunci da ya yanke a ranar Talata, mai shari'a Olabode Rhodes-Vivour ya bayyana cewa har rana mai kama da ta yau, babu laifi a gudanar da zaman kotu a yanar gizo.

Kwamitin kotun koli da ya kunshi mutane bakwai ya dauki wannan mataki ne bayan da dukkanin jihohin suka janye karar da suka shigar akan babban alkalin alkalai na kasa, Abubakar Malami da kuma majalisar tarayya.

Da duminsa: Kotun koli ta kori karar Lagos da Ekiti na haramta zaman kotu a yanar gizo
Harabar Kotun koli
Asali: UGC

Kotun kolin ta kuma yi gargadin cewa duk wani mai shari'a da yaki bin umurnin gudanar da zaman kotunsa a yanar gizo, to a shigar da kararsa ga majalisar shari'a NJC domin daukar mataki a kansa.

KARANTA WANNAN: Binciken badakalar EFCC: Magu ya sake bayyana gaban kwamiti

A wani labarin na Legit.ng, Kabir Akingbolu, lauya mai rajin kare hakkin bil adama, ya ce ministan shari'a, Abubakar Malami, ya na cikin hatsarin fuskanatar hukuncin daurin shekaru biyar bisa bayar da izinin siyar da gangunan man fetur mallakar gwamnatin tarayya.

Lauyan ya yi zargin cewa Malami ya bayar da umarnin sayar da kadarorin ne ba bisa ka'ida ba, bayan jami'an tsaro sun kwatosu daga hannun barayin man fetur a yankin Neja - Delta.

Wasu rahotanni sun wallafa wata takarda da ke nuna cewa Malami ya bayar da umarnin sayar da wasu manyan gangunan danyen man fetur ga wani kamfani bayan an kwacesu daga hannun barayin da ke fasa bututun NNPC.

Rahotannin sun bayyana cewa Malami ya bawa wani kamfani mai suna 'Omoh-Jay' umarnin sayar da danyen man fetur din da ke cikin gangunan duk da ana tuhumar kamfanin da zargin barnatar da metrik ton 12,000 na danyen man fetur a shekarar 2009.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel