Shugabannin tsaro basu bai wa Buhari kunya ba - Buratai

Shugabannin tsaro basu bai wa Buhari kunya ba - Buratai

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa shi da sauran shugabannin tsaro da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a shekaru biyar da suka gaba basu bashi kunya ba.

Suna kuma babban kokari wurin ganin sun sauke nauyinsu da aka dora musu, The Punch ta ruwaito.

Buratai ya yi wannan bayanin ne yayin da ya tarba shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Gabriel Olanisakin bayan da ya kai ziyara sansani na hudu na sojin kasa da ke Faskari a jihar Katsina.

Olanisakin ya kai ziyara sansanin ne don ganin yadda aikin atisayen 'Sahel Sanity' ke tafiya.

Buratai ya ce, "Yanzu shekaru 5 cif kenan da suka gabata. Ina Ndjamena, jamhuriyar Chadi a lokacin da naji sanarwar nadin Janar Olanisakin a matsayin shugaban ma'aikatan tsaro da nawa nadin.

"Muna godiya ga Allah da ya bamu lafiya mai inganci da muke shugabantar jami'an.

"Abun jin dadi ne mu sanar da shugaban kasar cewa muna matukar godiya a kan wannan karamcin kuma muna sake tabbatar da cewa ba za mu bashi kunya ba wurin sauke nauyin da ke kanmu.

"Ba za mu bai wa 'yan Najeriya kunya ba."

Buratai ya ce atisayen 'Sahel Sanity' ya fara dakile all'amuran 'yan bindiga da sauran miyagun laifuka a yankin arewa maso yamma bayan kwanaki kadan da aka kaddamar da shi.

Shugabannin tsaro basu bai wa Buhari kunya ba - Buratai
Shugabannin tsaro basu bai wa Buhari kunya ba - Buratai. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda na zazzabga wa ministan Buhari mari bayan ya neme ni da lalata - Nunieh

Ya kara da cewa, an kama wasu masu samar wa 'yan bindigar kayan aiki da masu kai musu bayanan sirri.

A jawabin Olanisakin, ya jinjinawa Buratai yadda yake mayar da rundunar sojin ta zamani.

Ya ce sansanin na hudu na dakarun sojin na daya daga cikin sabbin dabarun da aka fitar don shawo kan kalubalen tsaro na zamani.

A wani labari na daban, mayakan ta'addanci na Boko Haram sun kai hari wata babbar barikin sojoji da ke garin Maiduguri, a jihar Borno.

Majiya daga rundunar sojin ta sanar da jaridar The Cable cewa mayakan sun isa garin wurin karfe 11:20 na dare a ranar Litinin inda suka fara harbe-harbe zuwa cikin barikin.

Babu kakkautawa dakarun sojin suka fara mayar da martani amma sai dai tuni mayakan ta'addancin sun zagaye barikin, wata majiya ta tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel