Ministan Ilimi ya kaddamar da majalisun zartarwa na jami'o'i 13 a Najeriya

Ministan Ilimi ya kaddamar da majalisun zartarwa na jami'o'i 13 a Najeriya

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya kaddamar da majalisun zartarwa na jami’o’i 13 na tarayya da ke fadin kasar nan.

Ministan yayin bikin nadin da aka yi cikin birnin Abuja a ranar Litinin, ya nemi shugabanni da mambobin majalisu daban-daban da su inganta dangartaka mai kyau yayin aiwatar da aikinsu a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Ya bukaci mambobi da shugabannin majalisun da su mutunta bin doka da oda yayin sauke nauyin da rataya a wuyansu gami da kiyaye dokokin hukumar da'ar ma'aikata yayin nadin jami’ansu.

Ministan Ilimi; Adamu Adamu
Hoto daga jaridar The Punch
Ministan Ilimi; Adamu Adamu Hoto daga jaridar The Punch
Asali: Twitter

Ministan ya kuma hori majalisun da su toshe duk wata kafa ta tsiyayewar kudin shiga tare da bijiro da dabarun da za su bunkasa harkokin samun kudaden shiga a jami'o'in.

A cewarsa, babban kalubalen da jami'o'in kasar nan ke fuskanta shi ne rashin isasshen kudin gudanarwa da kuma rashin yin tattali yayin kashe-kashen kudi.

KARANTA KUMA: Makarantu masu zaman kansu sun roki Gwamnati ta sauya hukuncin hana zana jarrabawar WAEC a bana

Shi ma a nasa jawabin, Babban sakataren Hukumar da ke sa ido kan jami’o’i ta kasa (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed, ya ce wannan nadi da aka yi ya nuna mafarar wani sabon tsari na gabatar da jami’o’i 13 na musamman.

Farfesa Rasheed ya ce, Hukumar tana alfahari da tsarin taswirar da ta fitar tun daga 2018 zuwa 2020 domin himmatuwa wajen farfado da tsarin ilimin a jami'o'in kasar.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito, jerin jami'o'in da aka yi wa nadin sabbin majalisun zartarwa sun hadar da:

  1. Jami'ar Tarayya ta Lakwaja; Jihar Kogi
  2. Jami'ar Tarayya ta Lafia, Jihar Nasarawa;
  3. Jami'ar Tarayya ta Kashere, Jihar Gombe;
  4. Jami'ar Tarayya ta Wukari, Jihar Taraba;
  5. Jami'ar Tarayya ta Dutsinma, Jihar Katsina;
  6. Jami'ar Tarayya ta Dutse, Jihar Jigawa;
  7. Jami'ar Ndufo Alike, Jihar Ebonyi;
  8. Jami'ar Tarayya ta Oye-Ekiti, Jihar Ekiti;
  9. Jami'ar Tarayya ta Otuoke, Jihar Bayelsa;
  10. Jami'ar Tarayya ta Birnin Kebbi, Jihar Kebbi;
  11. Jami'ar Tarayya ta Gusau, Jihar Zamfara;
  12. Jami'ar Tarayya ta Gashua, Jihar Yobe;
  13. Jami'ar Tarayya ta nazarin kimiyar Lafiya ta Otukpo, Jihar Benuwe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel