Makarantu masu zaman kansu sun roki Gwamnati ta sauya hukuncin hana zana jarrabawar WAEC a bana

Makarantu masu zaman kansu sun roki Gwamnati ta sauya hukuncin hana zana jarrabawar WAEC a bana

Kungiyar NAPPS ta makarantu masu zaman kansu a fadin tarayya, ta magantu a kan matsayarsu ta buɗe makarantu domin komawa bakin aiki.

Kungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya tabbacin cewa, a halin yanzu dukkanin makarantu da ke karkashin jagorancinta, sun kammala duk wani shiri na komawa kan aiki.

NAPSS ta bukaci gwamnatin ta ba da umarnin buɗe makarantu domin bai wa ɗalibai damar komawa domin ci gaba da ɗaukan darussa.

Haka zalika kungiyar ta nemi gwamnatin ta sauya hukuncin da yanke na haramtawa ɗalibai a fadin kasar zana jarrabawar kammala karatun sakandire ta WAEC.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, kungiyar ta fi mayar da hankali wajen neman gwamnati ta bai wa ɗaliban makarantu masu zaman kansu damar zana jarrabawar WAEC a bana.

Wannan kiraye-kiraye gami da magiya da kungiyar ke yi ta biyo bayan sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi a Larabar makon da ya gabata na cewa daliban Najeriya ba za su zana jarrabawar WAEC ba a bana.

Ministan Ilimi Mallam Adamu Adamu
Hoto daga jaridar Premium Times
Ministan Ilimi Mallam Adamu Adamu Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar na kasa, Cif Yomi Otubela, shi ne ya bayyana shirin makarantun masu zaman kansu a ranar Litinin, inda ya bayar da tabbas kan la'akari da duk wasu matakai da mahukuntan lafiya suka shar'anta domin dakile yaduwar cutar korona.

Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta fito da sharuda na sake bude makarantu domin ‘daliban da ake shirin za su koma aji kwanan nan.

Sai dai gwamnatin kasar ba ta bayyana lokutan da ‘yan makarantan za su koma bakin karatu ba.

Tsare-tsaren da aka fito da su, su na kunshe da sharuda da matakai da ake bukata kafin a iya daukar darasi ko shiga aji a lokacin annobar COVID-19.

KARANTA KUMA: 'Yan APC 9 da ke fafutikar maye gurbin mataimakin gwamnan jihar Ondo

Kamar yadda ma’aikatar ilmi ta kasa ta bayyana a ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2020, za a rika ba da tazara a wurin karatu idan an bude makarantun boko.

Jawabin ya nuna cewa za a rika samun ratar akalla mita biyu tsakanin masu daukar karatu da ma’aikatan makaranta a cikin aji da sauran dakunan karatu.

Mai girma ministan ilmi, Mallam Adamu Adamu da karamin ministan ilmi na tarayya, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba su ka sa hannu a wannan takarda dazu.

Jaridar Punch ta ce ma’aikatar ilmi ta dauki wannan mataki ne tare da ma’aikatar muhalli, da ta lafiya, da kuma sauran masana kiwon lafiya a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel