'Yan APC 9 da ke fafutikar maye gurbin mataimakin gwamnan jihar Ondo

'Yan APC 9 da ke fafutikar maye gurbin mataimakin gwamnan jihar Ondo

- A yayin da ake shirin tsige mataimakin gwamnan Ondo, wasu jigogin jam'iyyar APC guda tara sun fara hankoron maye girbinsa

- Manyan jiga-jigan jam'iyyar da ke hankoron kujerar mataimakin gwamnan, sun kuma nuna sha'awarsu ta zama abokin takarar gwamna Akeredolu a zaben jihar mai zuwa

- A yayin da ake rige-rigen maye gurbin, babban alkalin jihar Ondo ya yi watsi da wata wasika ta neman kafa kwamitin bincike a kan mataimakin gwamnan

A yayin da ake ci gaba da fafutikar tsige mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajali, jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun nuna sha'awar maye gurbinsa.

Jerin jiga-jigan jam'iyyar da ke hankoron maye gurbin Ajayi a tsawon dan lokacin da ya rage a wa'adin mulkin gwamna Akerelodu na farko, sun kuma nuna sha'awar zame masa abokin takara a zaben jihar mai zuwa.

Babu shakka a ranar 10 ga watan Oktoba na 2020, za a gudanar zaben gwamnan jihar Ondo kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta fitar a tsare-tsarenta da kuma jadawali.

A halin yanzu akwai jiga-jigan jam'iyyar APC 9 da ke hankoron maye gurbin Ajayi a yayin da ake ci gaba da fafutikar tsige shi daga kujerar mataimakin gwamnan jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Ondo; Agboola Ajayi
Hakkin mallakar hoto; Jam'iyyar PDP
Mataimakin gwamnan jihar Ondo; Agboola Ajayi Hakkin mallakar hoto; Jam'iyyar PDP
Asali: Twitter

Jaridar Guardian a ruwaito cewa, masu takarar neman maye kujerar mataimakin gwamnan su na amfani da duk wani tasiri da suke da shi wajen tabbatar da an tsige Ajayi daga mukaminsa.

Jerin manyan jam'iyyar 9 da suka nuna sha'awar maye gurbin Ajayi kamar yadda rahotanni suka tabbatar sun hadar da:

1. Mrs Oladunni Odu, (Tsohuwar kwamishinan Ilimi na jihar)

2. Dr Paul Akintelure, ( Shugaban hukumar ilimi na bai daya ta jihar)

3. Femi Agagu, (Kwamishinan Ilimi)

4. Lucky Ayedatiwa

5. Gbenga Edema

6. Olamide Falana

7. Jimi Kuforiji, (Mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Ondo)

8. Wale Akinterinwa, (Kwamishinan Kudi)

9. Yetunde Adeyanju, (Kwamishinan Ruwa).

KARANTA KUMA: Rasha ta zama kasa ta farko da ta kammala gwajin rigakafin cutar korona

A yayin da ake ci gaba da neman wanda zai maye gurbin Mista Ajayi, Mai Shari'a Oluwatoyin Akeredolu, ta yi watsi da wasika da aike mata wadda ta nemi ta kafa kwamitin bincike a kan mataimakin gwamnan.

Wasikar wadda majalisar dokokin jihar ta aike wa Babbar Alkalin jihar, ta bukaci kwamitin da za a kafa ya gudanar da bincike kan zargin aikata ba daidai ba da ake yi wa mataimakin gwamnan.

A ranar Alhamis 9 ga watan Yuli ne kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Bamidele Oleyelogun, ya aike da wasikar wadda ta bukaci a kafa kwamitin mutum bakwai da za su titsiye Mista Ajayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel