Rasha ta zama kasa ta farko da ta kammala gwajin rigakafin cutar korona

Rasha ta zama kasa ta farko da ta kammala gwajin rigakafin cutar korona

Rasha ta zama kasa ta farko da ta kammala gwajin rigakafin cutar Covid-19, bayan da Jami’ar Sechenov ta ce ta kammala nazari da bincike a kan allurar rigakafin cutar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Rasha TASS ya ruwaito cewa, wannan yana kunshe cikin sanarwar da cibiyar nazari da bincike a kan kiwon lafiya ta Jami'ar Sechenov ta fitar a yau Litinin.

Shugabar cibiyar nazarin kiwon lafiya ta Jami'ar, Elena Smolyarchuk, ta ce binciken da aka gudanar kan rigakafin ya yi tasirin a kan mutanen da aka yi gwajin a kansu.

Kamfanin dillancin labaran ya nakalto Smolyarchuk tana cewa: "An gama binciken kuma an tabbatar da cewa ingancin maganin. Za a sallami wadanda aka yi gwajin a kansu a ranar 15 ga Yuli da 20 ga Yuli."

Shugaban China da takwaransa na Rasha
Hakkin mallakar hoto; Al Jazeera
Shugaban China da takwaransa na Rasha Hakkin mallakar hoto; Al Jazeera
Asali: Twitter

"Daga yanzu har zuwa lokacin da za a sallami mutanen da su ka bayar da kansu domin yin gwaji, a a ci gaba da sanya ido da lura a kansu. Kuma bayan haka za su rika zuwa ana duban lafiyarsu a kai-a kai"

A watan da ya gabata ne gwamnatin Rasha ta ba da lamunin aiwatar da gwaji kan wasu allurar rigakafi biyu, domin tabbatar da tasirinsu wajen magance cutar korona.

Mujallar Clinical Trials ta ruwaito cewa, Cibiyar Gamaleya mai nazari da bincike a kan kwayoyin cututtuka ta kasar Rasha, ita ta hada wannan magunguna biyu da a yanzu aka kammala gwaji a kansu.

KARANTA KUMA: Za mu kashe N3bn domin yakar zazzabin cizon sauro a Kano - Ganduje

An gwada maganin da ke cikin nau'in ruwan allura a Asibitin Dakaru na Burdenko, yayin da Jami'ar Sechenov ta tantance maganin a cikin nau'insa na gari wanda za a yi hadawa ya koma ruwan allura ta tsirawa a jiki.

Jami'ar ta fara gwajin maganin a mataki na farko a ranar 18 ga watan Yuni kan mutane 18. Sai kuma a ranar 23 ga watan Yuni da aka yi gwajin a mataki na biyu kan mutane ashirin.

Gabanin aiwatar da gwajin rigakafin a kan mutane, an fara gwada ta a kan manya da ƙananan dabbobi domin tantance illar yawan gubar da ta kunsa, tasiri da kuma aminci a gudanar a Ma'aikatar Tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel