Yadda na zazzabga wa ministan Buhari mari bayan ya neme ni da lalata - Nunieh

Yadda na zazzabga wa ministan Buhari mari bayan ya neme ni da lalata - Nunieh

Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktan hukumar kula da habaka yankin Neja Delta (NDDC), ta ce ta zabga wa Goodwill Akpabio, tsohon ministan kula da al'amuran Neja Delta, mari sakamakon neman yin lalata da ita da yayi.

A yayin zantawa da gidan talabijin na Arise, Nunieh ta ce al'amarin ya faru ne a gidan saukar bakin ministan da ke Abuja.

Ta ce martanin da tayi masa yayin da ya nemi yin lalata da ita na nuna cewa bata daukar wulakanci a matsayinta na 'yar asalin jihar Ribas.

"Me yasa bai sanar da cewa na maresa ba a gidan saukar bakin sa da ke Apo? Ni ce mace daya da ta taba marin Akpabio. Ya yi kokarin yin lalata dani," tace.

Ta kara da cewa, "Na zabga mishi mari. Daga Ogoni nake kuma ba a wasan banza da mu. Na nunawa Akpabio cewa matan jihar Ribas basu daukar wulakanci."

Tsohuwar shugaban NDDC ta zargi Akpabio da kara kudin kasafin hukumar.

Ta ce ministan ya umarceta da saka wasu ayyuka na hukumar 'yan gudun hijira a cikin kasafin kudin NDDC.

Yadda na zazzabga wa ministan Buhari mari bayan ya neme ni da lalata - Nunieh
Yadda na zazzabga wa ministan Buhari mari bayan ya neme ni da lalata - Nunieh. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Magu ya bayyana matakin da zai dauka saboda tsaresa da aka yi na kwanaki

"Akpabio ya rubuta min jerin wasu ayyuka na hukumar 'yan gudun hijira don sakawa a kasafin kudin NDDC," tace.

Nunieh da Akpabio suna ta jifan junansu da zargi daban-daban bayan bayyana bincikarsu da ake a kan wasu kudin hukumar har N40 biliyan.

Ta zargi cewa, Akpabio ya bukaceta da ta canja dalolin da ke asusun bankin NDDC zuwa Naira, ta kori shugaban tawagar lauyoyin hukumar wanda dan arewa ne.

Sannan cewa ta cire dukkan daraktocin da suka ki bin umarninsa tare da yi wa Peter Nwaoboshi sharri.

Kamar yadda Nunieh tace, Akpabio ya ja mata kunne da cewa idan bata aikata abinda yake so ba zai tsigeta.

Ta kara zargin Akpabio da cewa, baya taba sa hannunsa a kan wata takarda sai dai ya sa mukarrabansa su yi damfara.

Ta ce ministan ya bukaceta da ta yi rantsuwar sirri don ya hanata fallasa shi amma ta ki.

"A ranar farko da muka hadu muna hanyar tafiya rantsarwa, ya ce min idan har ban yi abinda yake so ba, zai koreni ba tare da jinkiri ba," tace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel