Magu: Falana ya yi barazanar shigar da karar wata jarida cikin sa'o'i 48

Magu: Falana ya yi barazanar shigar da karar wata jarida cikin sa'o'i 48

- Shahararren lauya Femi Falana (SAN) ya yi barazanar shigar da karar jaridar The Nation cikin sa'o'i 48

- Falana ya zargi jaridar da wallafa labarin da ya alakanta shi da Naira miliyan 28 daga cikin kudaden da ake zargin Ibrahim Magu ya handame

- Jaridar ta wallafa labarin a ranar 12 ga watan Yuli, 2020, labarin da Falana ya kira karya tsagoronta

Shahararren lauyan nan na Nigeria kuma mai kare hakkin bil'Adama, Femi Falana (SAN) ya baiwa jaridar The Nation wa'adin awanni 48 da ta rubuta masa wasikar ban hakuri, tana mai amincewa da cewar labarin da ta wallafa a shafinta na farko akansa karya ne tsagoronta.

Falana ya bayar da wannan wa'adin ne ta hannun CITIPOINT, wani ofishin lauyoyi da ke da zama a Lagos. Barazanar wacce ke a cikin shafuka uku ta hakaito taken labarin da jaridar ta wallafa da, "Magu na fuskantar wani babban kalubale yayin da sabbin alkaluma suka sake bayyana kan kudaden satar da aka kwato."

Jaridar ta wallafa labarin a ranar 12 ga watan Yuli, 2020, a inda kafar watsa labaran ta alakanta Femi Falana da Naira miliyan 28 daga cikin kudaden da ake zargin tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya handame.

KARANTA WANNAN: Buhari ya taya Usman murnar zama shagon gasar damben UFC

Magu: Falana ya yi barazanar shigar da karar wata jarida cikin sa'o'i 48
Magu: Falana ya yi barazanar shigar da karar wata jarida cikin sa'o'i 48
Asali: UGC

Ofishin lauyoyin ya yi nuni da cewa labarin da abunda ya kunsa ya bata sunan Femi Falana (SAN) a idon duniya, domin haka, gaza cika bukatun wanda suke karewa zai tilasta ofishin daukar maganar zuwa kotu domin bin kadin al'amarin.

A wani labarin kuma, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa, Wasu daga cikin kawayen kasar Nigeria da ke yaki da cin hanci da rashawa sun kara sa kaimi wajen sa ido kan tuhumar da ake yiwa shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu, wanda a halin yanzu yake karkashin dakatarwa.

Manyan kasashe wadanda wasunsu ke da kyakkyawar alaka ta fuskar shari'a da Nigeria, na sa ido kan yadda ake gudanar da bincike da kuma shari'ar badakalar, kamar yadda rahotanni suka bayyana a karshen makon da ya gabata.

Kasashen sun hada da Amurka, Burtaniya, hadakar kasashen Labarabawa (UAE), Faransa da kuma Switzerland.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng