Gwamna Ganduje ya yaba wa Gwamnatin Tarayya a kan inganta wutar lantarki a Kano

Gwamna Ganduje ya yaba wa Gwamnatin Tarayya a kan inganta wutar lantarki a Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya yabawa Gwamnatin Tarayya a kan kafa wata katafariyar tashar samar da wutar lantarki a karamar hukumar Bichi domin bunkasa samuwar wutar lantarki a jihar.

Hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan sadarwa da hulda da jama'a na gwamnan, Malam Ameen Yassar ya fitar.

Ganduje ya yi wannan yabon ne yayin da yake karbar bakuncin Shugaban Kamfanin rarraba wutar lantarki (TCN), Alhaji Sule AbdulAziz, wanda ya ziyarce fadar gwamnatinsa da ke birnin Kanon Dabo.

Kamar yadda Gidan Talabijin na kasa NTA ya ruwaito, gwamnan ya ce wannan katafaren aiki zai kawo ci gaba da habakar tattalin arziki a jihar bayan gushewar annobar korona.

Gwamna Ganduje
Hakkin mallakar hoto: @ShuwakiYusuf
Gwamna Ganduje Hakkin mallakar hoto: @ShuwakiYusuf
Asali: Twitter

Ganduje ya yi godiya ga shugaba Muhammadu Buhari da kuma Ministan Lantarki da suka jajirce a kan taimakawa jihar wajen farfado da tattalin arzikinta, musamman ma bayan an gama da kalubalen cutar korona.

A sanarwar da Malam Yassar ya fitar, wannan aiki zai bunkasa samuwar wutar lantarki a kananan hukumomi bakwai da ke makwabtaka da karamar hukumar Bichi, lamarin da zai habaka harkokin kasuwanci a cikinsu.

A nasa jawaban, Alhaji Abdulaziz ya ce ya ziyarci jihar Kano domin sa ido kan ayyukan kafa tashar samar da wutar lantarki, inda ya bayyana gamsuwa da irin goyon bayan da gwamnatin jihar ta bayar.

KARANTA KUMA: WAEC: Iyayen dalibai za su gana da gwamnatin tarayya a ranar Litinin

A baya bayan nan ne kamfanin KEDCO mai rarraba wutar lantarki na Kano, ya ce abokanan huldarsa da ke shiyyar Kano za su samu karin wutar lantarki a yayin da kamfanin ya inganta harkokinsa na gudanarwa.

KEDCO ya yi wannan sanarwa ne bayan da kamfanin TCN ya kammala a layin samar da wutar lantarki na Shiroro-Mando, wanda ke samar da hasken lantarki ga al'ummar Kano da kewaye.

Wannan sanarwa tana kunshe ne cikin wata takarda da mai magana da yawun kamfanin KEDCO, Ibrahim Sani Shawai ya sanya wa hannu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel