WAEC: Iyayen dalibai za su gana da gwamnatin tarayya a ranar Litinin

WAEC: Iyayen dalibai za su gana da gwamnatin tarayya a ranar Litinin

Kungiyar iyayen dalibai da malamai ta kasa NAPTAN, ta fadi halin da ta shiga biyo bayan furucin da ministan ilimi Adamu Adamu ya yi dangane da zana jarabawar WAEC a bana.

NAPTAN ta ce har yanzu ba ta san manufar furuncin da ministan ya yi ba na cewa dalibai a fadin kasar nan ba za su zana jarrabawa kammala karatun sakandire ta WAEC ba a bana.

Kungiyar ta shiga cikin rudani da rashin fahimtar hukuncin da gwamnatin tarayyar kasar nan ta yanke game da batun jarrabawar wadda a kayyade za a fara gudanar da ita a ranar 4 ga watan Agusta.

Wannan furuci ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar NAPTAN na kasa, Alhaji Haruna Danjuma, yayin da yake zantawa da manema labarai na jaridar The Punch tun a ranar Alhamis.

Alhaji Danjuma ya ce kungiyar ta yanke shawarar garzaya wa har gaban ministan a ranar Litinin, inda za su tattauna domin cimma matsaya da neman mafita.

Mallam Adamu Adamu
Hoto daga jaridar Premium Times
Mallam Adamu Adamu Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: UGC

A makon karshe na watan Mayun da ya gabata ne kungiyar NAPTAN ta nemi gwamnati da ta ba da umarnin bude makarantu ga daliban da shirin zana jarrabawar WAEC da kuma NECO.

Kungiyar ta sanar da cewa ta ce iyaye sun ƙuduri aniyar yin aiki tare da makarantu don sanya matakai kamar su samar da takunkumin rufe fuska, botikan wanke hannu don rage haɗarin kamuwa da cutar a tsakanin ɗalibai.

Da yake martani dangane da umarnin ministan ilimi wanda ya furta cewa ba zai yiwa dalibai su zana jarrabawar WAEC a bana ba, Danjuma ya ce sam ba za ta sabu ba, da wannan suka bukaci ganawa da gwamnati a kan lamarin.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa aka daina bincike kan faifan daloli na Ganduje - Muhuyi Rimin Gado

A Litinin ta makon da ya gabata ne karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba ya sanar da cewa, za a gabatar da jarrabawar WAEC ta bana daga ranar 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga Satumba.

Sai kuma daga bisani a ranar Laraba, Mallam Adamu ya sanar da cewa makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe kuma babu batun zana jarrabawar WAEC a bana.

Ya kuma umarci gwamnatocin jihohi da suka ba da sanarwa bude makarantu da su gaggauta jingine aniyarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel