Mu tsamo nahiyar mu daga kangin rashawa - Buhari ya gargadi shugabannin Afrika

Mu tsamo nahiyar mu daga kangin rashawa - Buhari ya gargadi shugabannin Afrika

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira na gargadi ga shugabannin kasashen Afrika da su tashi tsaye wurjanjan domin tsamo nahiyar nan daga kangin rashawa.

Wannan gargadi yana kunshe cikin wata sanarwa da Femi Adesina, hadimi na musamman kan sadarwa da hulda da al'umma ga shugaban kasar ya fitar a ranar Asabar.

Adesina ya sanar da cewa, Buhari ya yi wannan kira ne cikin wata wasika da ya aikewa da shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Ramaphosa shi ne shugaban kungiyar kasashen nahiyar Afrika yayin tunawa da ranar yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaba Muhammadu Buhari
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana a kan binciken da ake yi wa dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin zagon kasa (EFCC).

A wata takarda da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman a fannin yada labarai ga shugaban kasar, ya yi bayanin dalilin da yasa ya aminta da dakatar da Magu.

"An samu korafi daban-daban a kan mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Bayan bincike na farko, an kira jami'an da ke karkashinsa inda aka bincikesu.

"A saboda haka aka kafa kwamitin bincike mai kiyaye dokokin hukumar.

"A duk lokacin da ake zargin shugaban wata hukuma, a kan bukacesa da ya dakata da aiiki don a samu damar yin bincike ba tare da wata matsala ba.

"EFCC bata dogaro da yanayin mutum, a don haka bata sassauta wa kowa. Dakatar da Magu kuwa ya bai wa hukumar damar sauke nauyinta ba tare da wani cikas ba.

KARANTA KUMA: Rashin zana jarrabawar WAEC a bana zai hana dalibai shiga jami'o'i - Farfesa Ayo

"EFCC na da zakakurai, jajirtattun ma'aikata maza da mata masu fatan kiyaye dukkan dokokin kasar nan tare da mika duk wanda ya zo da almundahana gaban hukuma.

"Amma kuma, an bai wa Magu damar da zai kare kansa tare da amsa tambayoyin da ake masa. Hakan ce kuwa ta kamata a karkashin dokar kasar nan wacce ta bai wa kowa damar kare kansa," takardar tace.

Garba Shehu ya kara da cewa, dole ne a gane cewa yaki da rashawa a kasar nan ba a wuri daya ake tsayawa ba. Ta kowanne fanni ana kokarin tabbatar da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel