Rashin zana jarrabawar WAEC a bana zai hana dalibai shiga jami'o'i - Farfesa Ayo

Rashin zana jarrabawar WAEC a bana zai hana dalibai shiga jami'o'i - Farfesa Ayo

Tun daga karshen watan Maris har kawo yanzu, dalibai a fadin Najeriya na ci gaba da zaman dirshan a gidajensu biyo bayan rufe makarantu da gwamnati ta yi saboda annobar korona.

Wannan lamari yana mayar da hannun agogo baya a sashen ilimi na kasar musamman ga wasu rukuni biyu na daliban da ke shirin zana jarrabawarsu ta kammala wani mataki na karatu.

Daga cikin rukunin daliban da wannan hukunci na rufe makarantu ya kawo wa cikas sun hadar da 'yan aji shida a makarantun firamare da ke shirin zana jarrabawar neman shiga sakandire (Common entrance).

Daya rukunin daliban da su ka yi gamo da tangarda su ne 'yan aji shida a makarantun sakandire da ke gab da fara zana jarrabawar kammala wannan mataki na karatunsu domin neman shiga jami'o'i.

Dalibai yayin zana jarrawabar WAEC
Hoto daga; Jaridar This Day
Dalibai yayin zana jarrawabar WAEC Hoto daga; Jaridar This Day
Asali: UGC

Wani kwararre kuma masani a bangaren ilimi, ya yi gargadin cewa, wannan lamari zai janyo mummunan sakamako muddin ba a bari ɗalibai sun rubuta jarrabawar kammala matakin karantuttukansu ba.

Jigo cikin jerin jarrabawowin ita ce wadda hukumar WAEC mai shirya jarrabawar kammala karantun sakandire ta Yammacin Afrika ke gudanarwa a fadin yankin.

A wannan mako ne ake sa ran jihohin da suka kunshi kasar Yarbawa a Najeriya, za su gana a tsakaninsu domin tattaunawa a kan makomar yaransu.

Jihohin za su tattauna domin tabbatar da cewa dalibai a yankin sun ci gaba da karatunsu tare da yin la'akari da hanyoyin dakile annobar korona wadda ta hana ruwa guda a fadin duniya baki daya.

KARANTA KUMA: Ba za mu bude makarantu ba har sai mun tabbatar da amincin aiwatar da hakan - Jihohin Arewa

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, muddin makarantu su ci gaba da kasancewa a rufe, dalibai na iya yin asarar zangon wannan shekara gaba dayansa su na zaman dirshan a gida.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, a ranar Talata 7 ga watan Yuli ne ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa, daliban Najeriya ba za su zana jarrabawar WAEC ba a bana.

Farfesa Charles Ayo, tsohon shugaban jami'ar Covenant, ya ce idan har daliban Najeriya ba su zana jarrabawar ba a bana, to kuwa hakan zai haramta musu samun cancantar shiga jami'o'i da sauran makarantun gaba da sakandire.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel