Dokoki 3 da aka karya yayin auren dan ministan shari'a Malami

Dokoki 3 da aka karya yayin auren dan ministan shari'a Malami

Wasu kafofin watsa labarai sun tabbatar da cewa, masu farautar wanda suka saba wa shari'a a kasar nan sun keta doka yayin auren babban dan ministan shari'a kuma lauyan koli na kasa, Abubakar Malami.

An yi buduri na kece raini tun yayin da aka fara shagalin bikin a ranar Alhamis ta makon jiya, a Kanon Dabo, kuma za a karkare a Birnin Kebbi a mako mai zuwa.

A ranar Asabar ne dai aka daura auren Abdulazeez Abubakar Malami da kuma Amaryarsa, Khadija Abduljalil Danbatta, a masallacin Al-Furqan da ke Unguwar Nasararawa a Kanon Dabo.

Babu wani armashi a yayin daurin auren sakamakon dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta na kiyaye dokar bayar da tazara da kuma haramcin taron jama'a da ya haura na mutum ashirin.

Manyan kasar nan kalilan ne suka halarci daurin auren da suka hadar da gwamnonin Kano, Kebbi, Jigawa, Sakkwato, Zamfara da kuma Ministan Lantarki, Saleh Mamman.

Abdulazeez da Khadija
Hoto daga: @itz_azeyd
Abdulazeez da Khadija Hoto daga: @itz_azeyd
Asali: Instagram

Sauran manyan kasar da suka halarci taron sun hadar da; tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Goni Ali Modu, Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa, da Mele Kolo Kyari.

Sai dai wasu rahotanni da jaridar Sahara Reporters ta wallafa, sun nuna cewa, an saba ka'idodi da dama a wani rukuni na shagulgulan bikin da aka gudanar a Kano.

A wani faifan bidiyo da jaridar ta nuna, an yi facaka ta ruwan nairori da daloli yayin shagalin bikin da sunan likin kudi. Haka kuma babu wata tazara ko nesa-nesa da mutane suka yi ballantana sanya takunkumin rufe fuska.

Wannan likin kudi da aka yi ya sabawa dokar babban bankin Najeriya CBN mai kare martabar Naira, yayin da kuma aka sabawa dokokin da mahukuntan lafiya suka gindaya na dakile yaduwar cutar korona.

KARANTA KUMA: Kada a hana dalibai zana jarrabawar WAEC a bana - Majalisar Wakilai

Ba a nan ta tsaya ba, an ruwaito cewa, ministan ya sayawa dan nasa wani gida na alfarma na naira miliyan 300 a birnin Abuja, inda zai zauna da amaryarsa.

Sai dai daga bisani cikin wata sanawarwa da kakakin ministan, Umar Gwandu ya fitar, ya musanta zargin mallakar wannan gida. Ya ce sam dan ministan ma ba ya da niyyar zama a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel