Da duminsa: Wani ministan Buhari ya killace kansa

Da duminsa: Wani ministan Buhari ya killace kansa

Kwanaki kadan bayan tabbatar da cewa ministan al'amuran waje, Geoffrey Onyeama, ya kamu da cutar korona, wani ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake kamuwa da cutar.

Ministan al'amuran 'yan sanda, Muhammad Dingyadi shine ministan da ya harbu da kwayar cutar kuma tuni ya killace kansa bayan haduwa da ya yi da Onyeama a ranar Alhamis ta makon jiya.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin ma'aikatar kula da al'amuran 'yan sandan, Seyi Odutayo, ya tabbatar da wannan ci gaban ga jaridar Daily Nigerian a ranar Talata.

Kamar yadda Odutayo ya sanar, Dangyadi da kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wammako, sun hadu da Onyeama a ranar Alhamis ta makon da ya gabata.

Ya ce, "Ministanmu ya gana da takwaransa mai kula da ma'aikatar al'amuran harkokin waje a makon da ya gabata.

"Bayan sanarwar cewa Geoffrey Onyeama na dauke da cutar, ministan harkokin 'yan sandan ya yanke shawarar killace kansa don kiyaye dokokin hukumar yaki da cutuka masu yaduwa."

Da duminsa: Wani ministan Buhari ya killace kansa
Da duminsa: Wani ministan Buhari ya killace kansa. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Wata sabuwa: Ana bincikar Magu a kan mallakar kadarori a Dubai

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta tsawaita lokacin fara tashi da saukar jiragenta zuwa kasashen ketare har zuwa watan Oktoban 2020.

Hukumar kula da sufirin jiragen sama mai zaman kanta ta Najeriya (NCAA) ta sanar da masu ruwa da tsaki cewa an fasa bude tashi da saukar jiragen saman zuwa kasashen ketare a ranar 19 ga watan Augusta.

Gwamnatin tarayya ta dakatar da tashi da saukar jiragen sama zuwa kasashen ketare a watan Maris bayan barkewar annobar korona amma ta bude tashi da saukar jiragen a cikin gida.

Amma kuma kamfanoni da masu ruwa da tsaki sun ci gaba da matsanta wa gwamnati a kan ta dage dokar hana sauka da tashin jiragen saman zuwa kasashen ketare.

"Gwamnatin tarayya ta tsawaita lokacin bude filayen sauka da tashin jirage zuwa kasashen ketare.

"Amma kuma, NCAA ta ce za a iya mika bukata ta musamman a kan hakan kuma ta yuwu a amince. Za a mika wannan bukatar ga ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika." Kyaftin Musa Nuhu ya ce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel