ASUU ta fusata da yanayin ɗaukar ma'aikata masu yawa a jami'ar Bayero

ASUU ta fusata da yanayin ɗaukar ma'aikata masu yawa a jami'ar Bayero

Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU, ta soki tsarin da aka bi wajen ɗaukar ma'aikata masu yawan gaske a jami'ar Bayero da ke jihar Kano.

ASUU ta yi tir wannan yanayi na ɗaukar ma'aikata masu yawa a jami'ar ta Bayero kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Yuli, wadda kungiyar ta aikewa da shugaban jami'ar, ta yi zargin cewa tsarin da aka bi wajen na ɗaukar ma'aikata a jami'ar ya sabawa ka'ida.

Kungiyar ASUU reshen jami'ar ta fusata a kan yadda a baya bayanan nan aka rika ɗaukar ma'aikata masu yawan gaske ba tare da an bi tsarin da ya dace ba.

Jami'ar Bayero ta Kano
Hakkin mallakar hoto; Daily Trust
Jami'ar Bayero ta Kano Hakkin mallakar hoto; Daily Trust
Asali: UGC

Ta yi zargin cewa, babu adalci a tsarin da jami'ar ta shimfida wajen ɗaukar ma'aikatan domin kuwa an yi shi ne a sirrance ba tare da bai wa macancanta damar gwada sa'ar su ba.

A cikin wasikar, kungiyar ASUU ta ce babu adalci a tsarin da aka yi amfani da shi wajen ɗaukar ma'aikatan kuma yana cin karo da ka'idodin ɗauka da kuma ɗaga likafar ma'aikata da jami'ar tanada.

ASUU ta kara da cewa hanyar da aka bi wajen ɗaukar ma'aikatan ta karya ka'idojin da mahukuntan lafiya suka shar'anta na dakile yaduwar cutar korona wadda suka haramta yin tarurrukan jama'a da bai zama tilas ba.

KARANTA KUMA: Shari'ar layin wayar Hanan Buhari: Kotu ta yi fatali da karar DSS

A cewarta, rashin gaskiya ta mamaye gaggawar da aka yi wajen ɗaukar ma'aikatan a yayin da wasikun ɗaukan aikin suka nuna cewa an ɗauki ma'aikatan ne tun a watan Fabrairun 2019.

Ta yi gargadi ga mahukuntan jami'ar da cewa wannan lamari zai iya dakusar da martabar jami'ar tare da janyo koma baya da rusa duk wata ganuwa da lalacewar tsarin ilimi da ta ke da shi.

A yayin da ta ke gargadin jami'ar da ta guji aiwatar da irin wannan lamari na cin zarafin kanta, kungiyar ta bai wa shugaban jami'ar wa'adin kwanaki bakwai ya gabatar da duk wasu bayanai na tsarin da aka bi wajen ɗaukar ma'aikatan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel