COVID-19: Za mu sanya wa kananan hukumomi 11 ido - PTF

COVID-19: Za mu sanya wa kananan hukumomi 11 ido - PTF

Kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa a ranar Litinin, ta sanar da cewa za ta sa wa kananan hukumomi 11 ido saboda yadda cutar korona ke yaduwa a cikinsu.

Kwamitin ya ce zai mayar da hankali wurin kai dauki ga kananan hukumomon 11.

An zabi kananan hukumomin ne saboda yawan masu kamuwa da cutar coronavirus a cikinsu duk mako.

Mashiryin PTF, Dr Sani Aliyu ya ce: "Idan za a yi gwajin cutar coronavirus a kananan hukumomin, za a iya samun kashi 40 zuwa 50 masu cutar. Wannan ke nuna cewa ba a gwada yawan da ya dace.

"Amma kuma idan yawan masu cutar ya gaza kashi 10, hakan na nufin cewa ana gwajin yadda ya dace.

"Idan muka duba hakan muka hada da sharudda 3, akwai kananan hukumomin da suka cike sharuddan.

"A halin yanzu, mun gano kananan hukumomi 11 da za mu fara aiki a kai. Muna fatan samun canji nan da gajeren lokaci.

"Daga nan sai mu sake diban wasu sabbin kananan hukumomi bayan mun kammala da na farkon. Hakan ne sabon tsarin da za mu bi."

COVID-19: Za mu sanya wa kananan hukumomi 11 ido - PTF
COVID-19: Za mu sanya wa kananan hukumomi 11 ido - PTF. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Alkali ya daure ma'auratan da suka kafa wa 'yar aiki kusa a kai, konata da kuma saka mata makami a gaba

A wani labari na daban, kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa ya ce akwai yuwuwar gwamnatin tarayya ta sake garkame wasu kananan hukumomi 18 a fadin kasar nan saboda su ke da kashi 60 na masu cutar korona a Najeriya.

Shugaban kwamitin yaki da annobar korona ta kasa, Boss Mustapha, ya bayyana wannan alamari a tattaunawar da yayi da jaridar The Punch tare da sauran manema labaran gidan gwamnati.

Ya zanta da su ne bayan jagorar da yayi wa sauran mambobin kwamitin don tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin.

Mustapha, wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, ya ce kananan hukumomin da al'amarin ya shafa za su shiga wani sabon tsarin kulle.

A yayin jaddada cewa kasar nan bata kai kololuwa ba dangane da annobar korona, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa an kiyaye duk hanyoyin dakile cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel