Rundunar Sojin kasa ta ragargaji mayakan Boko Haram a Damboa

Rundunar Sojin kasa ta ragargaji mayakan Boko Haram a Damboa

A ci gaba da fafutikar karar da 'yan tsirarun mayakan Boko Haram da suka rage, rundunar LAFIYA DOLE, ta sake nuna fifikon bajinta a kan masu tayar da kayar bayar a jihar Borno.

A yunkurin da rundunar ta musamman ke yi na kakkabe masu tayar da zaune tsaye a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, ta kaddamar da wani sabon aiki mai suna Operation KANTANA JIMLAN.

Wannan sabon aikin hadin gwiwa da rundunar sojin ta kaddamar wani bangare na Operation LAFIYA DOLE da ta saba gudanarwa a yankin na Arewacin Kasar.

Rahoton hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar dakarun sojin kasa ta Najeriya ta fitar kan shafinta na dandalin sada zumuta a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli.

Rundunar Sojin kasa yayin kakkabe masu tayar da kayar baya a Arewa maso Yammacin Najeriya
Hakkin Mallakar hoto; Rundunar Dakarun tsaro ta kasa
Rundunar Sojin kasa yayin kakkabe masu tayar da kayar baya a Arewa maso Yammacin Najeriya Hakkin Mallakar hoto; Rundunar Dakarun tsaro ta kasa
Asali: Twitter

Rundunar ta sanar da cewa, a wani kicibus da ta yi da mayakan Boko Haram a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri, 'yan ta'adda 17 sun bakunci lahira.

Haka zalika ta sanar da cewa, wasu da dama daga cikin 'yan kungiyar masu tayar da kayar bayan sun tsere da raunuka daban-daban na harbin harsashi.

A yayin jaddada gagarumar nasarar da dakarun sojin suka samu yayin wannan artabu a ranar Talata, an kuma tsinto miyagun makamai da mayakan suka zubar yayin neman ta kansu.

Da ya ke karar kwana babu inda ba ta kai ziyara, rundunar sojin kasan ta yi rashin sa'a yayin da wasu dakaru biyu suka sadaukar da rayukansu wajen kare martabar kasar nan.

Haka kuma wasu dakarun hudu sun jikkata yayin fafatawa da mayakan na Boko Haram a filin daga.

KARANTA KUMA: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa

Da wannan rundunar take kira ga al'umma a kan kada su tashi hankulansu tare da neman su ci gaba da kiyaye doka yayin gudanar da al'amuransu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.

Yayin bayar da tabbacin daukar duk wani mataki na bai wa al'umma kariya, rundunar sojin ta ce a koda yaushe akwai dakaru da ke cikin shiri da jiran tsammanin mayar da martanin duk wani hari da 'yan ta'adda za su kawo.

A karshe, shugaban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya yaba wa gwarazan dakarun da suka nuna bajinta da kwarewar aiki wajen kakkabe masu tayar da zaune tsaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel