Covid-19: 'Yan Najeriya 25 sun maka gwamnatin China a kotu

Covid-19: 'Yan Najeriya 25 sun maka gwamnatin China a kotu

- 'Yan Najeriya 25 sun maka gwamnatin China da sauran cibiyoyi a gaban kuliya

- A cikin karar da suka shigar ta hannun lauyoyinsu, masu neman hakkin sun ce gwamnatin China ta yi rikon sakainar kashi kan lamarin da ya janyo bullar annobar korona

- Sun nemi a biya su dala biliyan 200 a matsayin diyyar duk wani halin kunci da yaduwar annobar korona ta janyo musu

Yayin da adadin mutanen da cutar korona a Najeriya suka haura 29,000, wasu 'yan kasar guda 25, sun maka gwamnatin China a kotu, su na neman ta biya su diyya sakamakon sanadin barkewar da yaduwar annobar da ta yi.

Tun fil azal, a garin Wuhan na kasar China, aka fara samun bullar cutar korona karo na farko yayin da shekarar 2019 ke shirin karkarewa.

A halin yanzu akwai fiye da mutum miliyan 11.7 da cutar ta harbi a fadin duniya cikin watanni tara da bayyanarta.

Fiye da kasashe da yankuna 200 annobar cutar ta shafa, lamarin da ya jefa al'ummomin duniya cikin ibtila'i da matsin tattalin arziki.

Shugaban China; Xi JinPing
Hoto daga livemint.com
Shugaban China; Xi JinPing Hoto daga livemint.com
Asali: UGC

Najeriya na daya daga cikin kasashen da annobar ta fi kamari a nahiyar Afrika, inda kasar Afirka ta Kudu da Ghana da kuma Aljeriya suke jan ragama ta fuskar yawan adadin mutanen da cutar ta harba a cikinsu.

Cikin karar da suka shigar ta hannun lauyoyinsu, masu neman hakkin sun ce gwamnatin China ta yi sakacin da ya janyo barkewa da yaduwar annobar korona a fadin duniya.

Sun ce tabbas akwai lauje cikin nadi domin kuwa irin yaudarar al'ummomin duniya da kasar China, ita ce ta yi sanadiyar yaduwar cutar har ya zuwa wannan lokaci.

KARANTA KUMA: 'Yan Fashin Daji: An tura karin ‘yan sanda 780 zuwa Zamfara

Damuwa da wannan lamari, a ranar Litinin, manema hakkin sun shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, da cewa kasar China ita ce ummul-aba-isin yaduwar wannan annoba.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa, wasu manyan lauyoyi 11 bisa jagorancin Farfesa Epiphany Azinge, su ne za su yi wakilcin shigar da wannan kara kan sakacin da gwamnatin China ta yi da take hakkin dan Adam.

Cikin 'yan kasar China da aka shigar da kararsu sun hadar da; Gwamnatin China, Ministan Shari'a, Cibiyar Ilimin Kimiya, Cibiyar Bincike da dakile Yaduwar Kwayoyin Cututtuka, Ministan Lafiya da sauransu.

Jerin masu shigar da karar sun hadar da: Kingsley Obioha, Shehu Mohammed Bello, Goodrand Nigeria Limited, Chief Ekene Ebuzeme, Prince Akin Oladipo, Sir Mark Olajide da Mr. Tanko Beji.

Sauran sun hadar da Ciff Victor Nwosa, Chidi Onwuemere, Kamfanin Tafiye-Tafiye na Pasaya, Trips Shop Limited, Susan Akporiaye, Carolyn Asoanya, Jerry Azinge, Williams Ezugwu, Ogugua Ogos da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel