Kasashe 5 mafi karfi a nahiyar Afrika

Kasashe 5 mafi karfi a nahiyar Afrika

- A kididdigar alkaluman da aka fitar kan kasashe duniya majiya karfi, kasar Masar ta fi kowacce a wannan fage a nahiyar Afrika

- Kasar Afrika ta Kudu, Kenya da Ghana, sun shiga cikin jerin kididdigar da aka fitar a mataki na biyu, uku da kuma na hudu a jere da juna

- A yayin da Najeriya ba ta samu shiga ba a jerin bajiman kasashe biyar na nahiyar Afrika da aka fitar, kasar Morocco ta zo a mataki na biyar

Cikin kiddigar kasashe da aka fitar a shekarar 2020, wasu kasashen Afrika biyar sun yi fice yayin da suka yi wa sauran kasashen nahiyar fintinkau ta fuskar karfi.

A jerin matsayi-matsayi na karfin kowace kasa da aka fitar a bana, kasar Masar wato Egypt, ta yi wa dukkanin sauran kasashen nahiyar zarra.

An fidda wannan kididdiga ne bisa la'akari da wasu dalilai da suka hadar da kare hakkin bil adama, karfin tattalin arziki, saukin gudanar da harkokin kasuwanci da sauransu.

A cikin jerin, kasar Masar ita ce ta farko a rukunin kasashen nahiyar Afirka yayin da ta zo a mataki na 36 a rukunin kasashen duniya.

Afrika ta Kudu ta zo a mataki na biyu cikin rukunin kasashen Afrika yayin da ta zo a mataki na 39 cikin rukunin kasashen duniya.

Ga jerin bajiman kasashe biyar maji karfi da suka yi wa sa'o'insu zarra a nahiyar Afrika:

1. Masar

2. Afrika ta Kudu

3. Kenya

4. Ghana

5. Morocco

Hoton kasar Masar, Kenya, Morocco da Ghana
Hakkin mallakar hoto; Atlas/thoughtco
Hoton kasar Masar, Kenya, Morocco da Ghana Hakkin mallakar hoto; Atlas/thoughtco
Asali: UGC

A wani rahoto mai nasaba da Legit.ng ta ruwaito, shafin nan na Africa Facts Zone, ya sake fitar da wata sabuwar kididdiga kan sha'ani da al'amuran da suka shafi kasashen nahiyar Afirka.

A wannan karo, shafin ya tattaro jerin kasashen nahiyar guda goma mafi samun wadataccen hasken wutar lantarki.

KARANTA KUMA: Hukumar WAEC ta fitar da jadawalin jarrabawar bana

Cikin jerin, kasar Mauritius da Tunisia sun ja ragamar kasashen da suka kere kowace kasa samun hasken lantarki dari bisa dari.

Haka nan kuma ba a bar kasar Masar, Algeria, Morocco da Seychelles a baya ba, inda sai an kai ruwa rana kafin hasken lantarki ya yi raurawa a kasashen.

A jerin kasashen guda goma, babu kasar da ke samun hasken lantarki na kasa da kashi 80 cikin dari.

Kasar Afrika ta Kudu da kuma Ghana, su ma sun shiga cikin sahun kasashen goma na nahiyar Afirka da su ka yi zarra ta fuskar wadatuwa da hasken wutar lantarki.

Ga dai jerin kasashen guda goma da kuma kashi na daidaituwar da hasken wutar lantarki ya yi kowanne daga cikin su:

1. Mauritius, Tunisia (100%)

3. Egypt (99.8%)

4. Algeria (99.1%)

5. Morocco (99%)

6. Seychelles (99%)

7. Cape Verde (96.1%)

8. Gabon (90.7%)

9. Ghana (84.3%)

10. Afrika ta Kudu (84.2%).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel