'Yan Fashin Daji: An tura karin ‘yan sanda 780 zuwa Zamfara

'Yan Fashin Daji: An tura karin ‘yan sanda 780 zuwa Zamfara

Hukumar jami'an tsaro ta 'yan sanda, za ta tura karin jami'anta 780 zuwa jihar Zamfara domin kara kaimi a fafutikar da ake yi na kawo karshen masu tayar da kayar baya a jihar.

Gwamnan jihar Muhammadu Bello Matawalle, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Juma'a cikin birnin Abuja.

Kamar yadda Gwamnan ya bayyana, sufeto janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu, shi ne ya bayar da amincewarsa a kan wannan lamari.

Yusuf Idris, Darakta Janar na sadarwa da hulda da al'umma ga gwamnan, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a babban birnin Zamfara, Gusau.

Shugabannin tsaro na Najeriya
Hoto daga fadar shugaban kasa
Shugabannin tsaro na Najeriya Hoto daga fadar shugaban kasa
Asali: UGC

Mista Idris ya ce Gwamna Matawalle ya samu wannan amincewa ne a yayin da ya ziyarci babban sufeton na 'yan sanda a hedikwatar rundunar a ranar Juma'a, 3 ga watan Yuli.

Ya ce daga cikin ma'aikatan da za a turo jihar za su kunshi jami'an rundunoni daban-daban ciki har da 'yan sanda masu jiran ko ta kwana, yaki da ta'addanci da kuma rundunan 'yan sanda ta musamman.

Hadimin gwamnan ya ce sabbin jami'an da za a turo za su hada karfi da karfe tare da ragowar 'yan sandan da ke jihar wajen kawar da 'yan tsirarun masu tayar da kayar baya da suka rage a jihar.

KARANTA KUMA: Babu sauran mai dauke da kwayoyin cutar korona a Jigawa - Dr. Zakari

Ya kara da cewa, gwamnan ya yi godiya ga gwamnatin tarayya da sauran hukumomin tsaro da ke fadi-tashin kawo karshen musibar da ta addabi jihar.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rayukan mutum uku sun salwanta a wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

Yayin harin na dare da 'yan bindigar suka kai a karshen makon da ya gabata, sun kuma yi awon gaba da shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar, Yusha'u Dissi tare da wata mata.

Haka zalika a wannan dare, 'yan bindigar sun kai hari wasu kauyuka na karamar hukumar Batsari ta jihar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A kauyen Dan Alhaji, 'yan bindiga sun bude wa mutanen kauyen wuta ta harsashin bindiga kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutum daya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel