Alkali ya daure ma'auratan da suka kafa wa 'yar aiki kusa a kai, konata da kuma saka mata makami a gaba

Alkali ya daure ma'auratan da suka kafa wa 'yar aiki kusa a kai, konata da kuma saka mata makami a gaba

Wata kotun majistare da ke jihar Enugu a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, ta bukaci a adana mata Jude Ozougwu da matarsa mai suna Ifeoma a gidan yari, sakamakon cin zarafin mai aikin su mai suna Nneoma Nnadi da ke da shekaru 10.

Rundunar 'yan sandan ta gurfanar da mata da mijin gaban alkali Agu da ke kotun majistare da ke zama a karamar hukumar Enugu ta arewa akan zarginsu da yunkurin kisan kai.

A yayin sauraron shari'ar, dan sanda mai gabatarwa, CSP Paschal Nwachukwu, ya musanta cewa da aka yi kotun bata da damar sauraron shari'ar.

Ya kara da cewa, maganar belin ma'auratan da aka nema tayi wuri, babu dalili kuma ya saba wa doka.

"Shaidun da aka mika gaban kotun sahihai ne kuma kwarara. Ta yaya za a kafa wa karamin yaro kusa a kai, a yi amfani da dutsen guga wurin konata tare da saka makami har a gabanta," ya sanar da kotun.

Amma kuma, lauyan ma'auratan, Emeka Orji, ya bukaci kotun da ta yi watsi da cece-kucen jama'a sannan ta bada belin. Orji ya ce ma'auratan na da yara kanana biyu wadanda suke kula dasu.

Mai shari'a Agu, ya ki amince wa da bada belin ma'auratan tare da bada umarnin adana su a gidan gyaran hali da ke Nsukka.

Alkali ya daure ma'auratan da suka kafa wa 'yar aiki kusa a kai, konata da kuma saka mata makami a gaba
Alkali ya daure ma'auratan da suka kafa wa 'yar aiki kusa a kai, konata da kuma saka mata makami a gaba. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An gayyaci Ibrahim Magu, shugaban EFCC amsa tambayoyi

A wani labari na daban, wani jami'in hukumar kula da cunkoson kan titi na jihar Legas, (LASTMA) mai suna Emmanuel Mekuri, ya sokawa karuwarsa da suke zaune tare wuka mai suna Patricia Ogunshola.

Hakan ta faru ne a yayin wani musu da suka fara a tsakaninsu a gidansa da ke Araromi, yankin Morogba ta jihar.

Jaridar Punch ta gano cewa, rikicin ya fara ne bayan zargin cin amana da ya shiga tsakaninsu wanda ya kai ga dambe.

Bayan fusatarsa, an zargi Emmanuel da daukar wuka inda ya sokawa Patricia a cinyarta ta dama amma bayan kasa jurewa, ta gudu ta bar gidan.

Daga nan, Emmanuel ya yi amfani da wukar inda ya sokawa kansa a ciki.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya ce diyar Patricia ce ta kira makwabta wadanda suka kira 'yan sanda. An samu gawar Emmanuel da wukar a inda aka aikata laifin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel