Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihohi umarnin bude makarantu

Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihohi umarnin bude makarantu

Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin ta shawarci gwamnatocin jihohi da su buɗe makarantu domin baiwa dalibai 'yan ajin karshe damar kammala shirye-shiryen zana jarrabawa.

Tun a watan Maris ne gwamnati ta ba da umarnin rufe kafatanin makarantu a fadin tarayyar kasar biyo bayan bullar cutar korona wadda a yanzu da ta harbi sama da mutum 25,000.

Gwamnatin Tarayyar ta ba da umarnin a buɗe makarantu ga wani rukuni na dalibai da suka hada da 'yan aji shida a makarantun Firamare, sai kuma 'yan aji uku da 'yan aji shida na makarantun sakandire.

Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona PTF
Hoto daga; Fadar shugaban kasa
Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona PTF Hoto daga; Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Har kawo yanzu gwamnatin ba ta fayyace ranar da 'yan aji shida na makarantun firamare za su fara jarabawar kwaman ba (Common entrance examination) da ranar fara jarabawar 'yan aji uku na makarantun sakandire (BECE).

Sai dai ta tabbata cewa, gwamnatin ta sanar da ranar fara jarabawar kammala karantun sakandire ta WAEC ga 'yan aji shida na makarantun sakandare.

Da wannan ne gwamnatin ta sanar da cewa a ranar Talata 7 ga watan Yuli, za a fara feshin magani a makarantu a yayin da dalibai ke shirin komawa ajujuwansu.

KARANTA KUMA: Rundunar 'Hadarin Daji' ta yi wa 'yan daban daji ruwan wuta a Zamfara da Katsina

Ministan zamantakewa da Muhalli, Muhammad Mahmood, shi ne ya sanar da hakan cikin birnin Abuja yayin zantawa da manema labarai kan al'amuran da suka shafi annobar korona.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Hukumar shirya jarrabawar kammala karantun sakandire ta yammacin Afrika (WAEC) ta sanar da ranar fara jarrabawar masu kammala sakandire na wannan shekarar.

Wannan sanarwar ta zo ne a yayin bayanin da kwamitin yaki da cutar korona ta fadar shugaban kasa (PTF) karkashin jagorancin sakataren gwamnatin kasar, ya yi a Abuja.

Kwamitin yaki da cutar korona ta kasa ya tabbatar da cewa za a gudanar da jarrabawar daga ranar 4 ga watan Augusta zuwa 5 ga Satumban 2020.

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba ne ya sanar da hakan a yayin taron.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter: "Gwamnantin tarayya ta sanar da cewa za a fara jarabawar WAEC daga ranar 4 ga watan Augusta zuwa 5 ga watan Satumba."

"Karamin ministan ilimi ne ya sanar da hakan a jawabin kullum na kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona a Abuja."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel