Zaben Edo: Ganduje da Buni sun isa ofishin APC domin karbar rantsuwa

Zaben Edo: Ganduje da Buni sun isa ofishin APC domin karbar rantsuwa

Shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, da kuma takwaransa na Kano, Abdullahi Ganduje, sun isa ofishin jam'iyyar na kasa domin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben gwamnan Edo.

Sauran wadanda suka ziyarci babbar sakateriyar jam'iyyar ta kasa da ke birnin Abuja, sun hadar da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, Sanata Andy Uba da sauransu.

A yayin zaben gwamnan Edo wanda za a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba, Osagie Ize-Iyamu, dan takara na jam'iyyar APC, zai gwabza da gwamnan jihar mai ci, Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP da kuma sauran 'yan takara.

Makonni kadan da suka gabata ne Gwamna Obaseki dai ya sauya sheka daga APC ya koma PDP, kuma jam'iyyar ta tsayar da shi takara ba tare da wata-wata ba.

Zaben Edo: Ganduje yayin zantawa da manema labarai a hedikwatar APC ta kasa
Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Punch
Zaben Edo: Ganduje yayin zantawa da manema labarai a hedikwatar APC ta kasa Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Punch
Asali: Twitter

Gwamna Ganduje wanda shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan na jam'iyar APC, ya ce babu abin da jam'iyyar adawa ta PDP ta sa gaba face ganin tana juya lalitar gwamnatin jihar Edo.

Furucin Ganduje ya zo ne yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin cikin sakateriyar jam'iyyar APC ta kasa da ke Abuja, jim kadan bayan an kaddamar da kwamitin yakin neman zaben gwamnan da zai jagoranta.

Ya kuma ce jam'iyyar APC ba ta damu da Gwamna Nyesom Wike ba, wanda zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar PDP saboda APC tana da dan takarar da ke da ikon lashe zaben farat daya.

KARANTA KUMA: An yi gobara a gidan wuta a jihar Kano

Legit.ng ta ruwaito cewa, kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP, a ranar Juma'ar da ta gabata, ya nada gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna a jihar Edo.

Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a kan shafinta na Twitter, inda ta bayyana gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a matsayin mataimakin kwamitin yakin neman zaben.

Wannan lamari ya faru ne kwana daya bayan da jam'iyyar APC ta nada gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar ta Edo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel