Har yanzu ba a sa ranar bude makarantu ba a Kano - Kwamishinan Ilimi

Har yanzu ba a sa ranar bude makarantu ba a Kano - Kwamishinan Ilimi

- Gwamnatin jihar Kano ta yi magana kan batun komawar daliban ajin karshe makarantu

- Kwamishinan ilimi na jihar ya ce za a hukunta duk wani malami da ya koma makaranta da sunan koyarwa

- Duk da gwamnatin tarayya ta ba da umarnin a bude makarantu ga wani rukuni na dalibai, gwamnatin Kano ta ce har yanzu ba ta sa ranar komawa ba

Gwamnatin jihar Kano ta yi magana dangane da jita-jitar da ke yaduwa a tsakanin al'umma na cewa a yau Litinin, 6 ga watan Yuli, za a bude makarantu ga wani rukuni na dalibai.

Legit.ng ta fahimci cewa, wasu daga cikin rukunin daliban da gwamnatin tarayya ta ba da umarnin a bude musu makarantu, sun shirya abinsu sun tafi makarantu da safiyar yau ta Litinin.

Sai dai fa sun riski makarantun a rufe, lamarin da ya sa a dole suka dawo gida ba bu shiri kuma ba tare da sun yi farin ciki a kan lamarin ba.

A yayin da 'yan kwanakin nan al'umma jihar Kano suka yi ta rade-radin za a bude makarantu a yau Litinin, wani gargadi da gwamnatin jihar ta yi ya disasashe duk wani tsammaninsu.

Kamfanin watsa labarai na Freedom Radio mai tushe a Kano, ya ruwaito cewa kwamishinan ilimi na jihar, ya ce za a dauki matakai masu tsauri ga duk makarantar da ta bude ba tare da umarnin gwamnatin ba.

Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

A yayin ganawarsa da manema labarai, Sanusu Sa'idu Kiru, ya ce babu shakka akwai hukunci mai girma da aka tanada ga duk wani malami da aka riska a cikin aji da sunan koyarwa.

Ya ce duk da cewa jihar Kano a kan sahu na gaba ta fuskar yawan dalibai da za su zana jarabawar kammala makarantun sakandire, amma har yanzu gwamnati ba ta tsayar da ranar da za a bude musu makarantun ba.

KARANTA KUMA: Zaben Edo: Gwamna Wike zai jagoranci kwamitin yakin neman zabe na jam'iyyar PDP

A ranar Litinin ne shugaban kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona PTF, Boss Mustapha, ya ba da sanarwar buɗe makarantu, domin ba wa 'yan azuzuwan karshe damar kammala shirinsu na zana jarrabawa.

Kwamitin ya ba da izinin bude makarantun domin 'yan aji shida na makarantun Firamare da kuma 'yan aji uku da aji shida na makarantun sakandire.

Sai dai kwamitin ya ba da wannan umarni bisa yarjejeniya kiyaye duk wasu ka'idodi da matakan dakile yaduwar cutar korona.

Duk da wannan umarni da gwamnatin ta bayar na sake buɗe makarantu, har yanzu jihohi na ci gaba da gwagwarmayar yanke hukunci kan ranakun sake buɗe makarantun.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatin Tarayya za ta gana da gwamnatocin jihohi a ranar Talata don tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen buɗe makarantun firamare da na sakandire ga 'yan ajin karshe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel