Yadda jami'in LASTMA ya sokawa karuwarsa wuka, ya kashe kansa

Yadda jami'in LASTMA ya sokawa karuwarsa wuka, ya kashe kansa

Wani jami'in hukumar kula da cunkoson kan titi na jihar Legas, (LASTMA) mai suna Emmanuel Mekuri, ya sokawa karuwarsa da suke zaune tare wuka mai suna Patricia Ogunshola.

Hakan ta faru ne a yayin wani musu da suka fara a tsakaninsu a gidansa da ke Araromi, yankin Morogba ta jihar.

Jaridar Punch fa gano cewa, rikicin ya fara ne bayan zargin cin amana da ya shiga tsakaninsu wanda ya kai ga dambe.

Bayan fusatarsa, an zargi Emmanuel da daukar wuka inda ya sokawa Patricia a cinyarta ta dama amma bayan kasa jurewa, ta gudu ta bar gidan.

Daga nan, Emmanuel ya yi amfani da wukar inda ya sokawa kansa a ciki.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya ce diyar Patricia ce ta kira makwabta wadanda suka kira 'yan sanda. An samu gawar Emmanuel da wukar a inda aka aikata laifin.

Ya ce an mika Patricia asibiti don samun magani yayin da aka mika gawar Emmanuel ma'adanar gawawwaki.

Yadda jami'in LASTMA ya sokawa karuwarsa wuka, ya kashe kansa
Yadda jami'in LASTMA ya sokawa karuwarsa wuka, ya kashe kansa. Hoto daga The Nation
Asali: Facebook

KU KARANTA: Maryam Sanda: Yadda wata mata ta yi hayar 'yan bindiga suka kashe mijinta

Elkana ya ce, "A ranar 5 ga watan Yulin 2020 wurin karfe daya, ofishin 'yan sanda da ke Morogbo sun samu kira daga yankin gidan Zoo na Araromi kan cewa wani jami'in LASTMA ya soki budurwasa da wuka a cinya.

"Diyar matar mai shekaru 13 ce ta sanar da makwabta. A bayanin yarinyar, ta ce Emmanuel ya yi yunkurin ci gaba da soka wa mahaifiyarta wuka amma sai ta bar dakin da gaggawa. Ta ce ya ci gaba da sokawa kansa wukar har hanjinsa suka bayyana inda ya mutu a take.

"Bayan isar jami'an, sun gaggauta mika ta asibiti don samun taimakon likitoci. A halin yanzu ta samu sauki kuma an mika gawarsa ma'adanar gawawwaki.

"Binciken farko sun nuna cewa masoyan sun fara zama da juna a watan Fabrairun 2020 amma basu yi aure ba."

Elkana ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Hakeem Odumosu ya bada umarnin mika al'amarin gaban sashen binciken manyan laifuka da ke Panti a Yaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel