Sace Yara daga Kano zuwa Kudu: Ganduje ya sake kafa kwamiti na musamman

Sace Yara daga Kano zuwa Kudu: Ganduje ya sake kafa kwamiti na musamman

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya kaddamar da kwamiti na musamman domin daukar mataki kan binciken diddigi da da Hukumar shari'a ta gudanar kan kwato hakkokin kananan yaran nan da suka bace daga jihar.

Ganduje ya sake kafa wani kwamitin mai kunshe da mutane 16 bisa jagorancin Jastis Wada Umar Rano da kuma Musa Bichi a matsayin sakatare.

Sauran mambobin kwamitin an zakulo su ne daga rassa daban-daban na kungiyoyin kare hakkin bil Adama masu zaman kansu da kuma na gwamnati.

Wannan kwamiti zai riki makama ta gaba bayan kammala bibiyar duk mutanen da aka sace a jihar tun daga shekarar 2010 kawo yanzu, ta hanyar jin ra'ayoyin da shaidu ta baka ko a rubuce.

Babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin Kano, Abba Anwar, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya gabatar a ranar Asabar cikin Kanon Dabo.

Yaran da aka sace a Kano
Hakkin mallakar hoto; Daily Nigerian
Yaran da aka sace a Kano Hakkin mallakar hoto; Daily Nigerian
Asali: UGC

Sanarwar ta nakalto Ganduje yana bayyana rahoton da kuma shawarwarin da hukumar ta gabatar a matsayin mai matukar muhimmanci, wanda ya kamata a aiwatar da shi don magance matsalar.

Gwamnan yayin sabunta dora nauyi a kan kwamitin, ya ce babu wanda ya dace ya yi aiki da shawarwarin gami da daukar mataki na gaba face 'yan kwamitin da suka gudanar da bincike a kan lamarin.

Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban shekarar da gabata ne Ganduje ya kaddamar da wani kwamiti bisa jagorancin Jastis Wada Rano domin bin diddigin kwato hakkin yaran da aka sace a jihar tun daga shekarar 2010.

KARANTA KUMA: Gobara ta ci mutum 16 a Kano

Ganduje ya yaba wa mambobin kwamitin bisa kyakkyawan aiki tare da lura da cewa wannan kwazo da suka yi shi ne dalilin ya sa tun farko a zabe su domin su jibinci lamarin.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a watannin karshe na shekarar da gabata, rahotanni sun yadu a kafofin sadarwa kan wasu yaran Kano da aka sace kuma aka ci kasuwarsu a jihar Anambra.

A wancan lokaci, an samu nasarar cafke wasu daga cikin mutanen da ake zargi da aikata wannan mummunan fasadi a bayan kasa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan sace yaran tare da raba su daga iyayensu, an kuma sauya musu addini daga na Musulunci zuwa Kiristanci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel