COVID-19: Yadda NAFDAC ta tarwatsa taron kaddamar da maganin korona na gargajiya

COVID-19: Yadda NAFDAC ta tarwatsa taron kaddamar da maganin korona na gargajiya

Jami'an hukumar tabbatar da ingancin Abinci da magungunan, (NAFDAC) sun tarwatsa taron kaddamar da wani maganin gargajiya na cutar korona a garin Abeokuta da ke jihar Ogun.

Wani mai maganin gargajiya mai suna Paul Oni ne ya yi yunkurin kaddamar da shi a ranar Alhamis a wani dakin taro da ke yankin Ake na babban birnin jihar.

Daga bisani, jami'an hukumar NAFDAC sun hana taron bayan da suka tsinkayi wurin tare da 'yan sanda da kuma jami'an tsaron fararen kaya.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa daga bisani jami'an sun bi Oni har kamfaninsa inda ya samar da maganin gargajiyar tare da garkameshi bayan kammala dubawa da suka yi.

Yayin bayani ga manema labarai bayan garkame kamfanin, Oni ya koka da yawan masu cutar korona a fadin kasar nan.

Ya jajanta yawan kudin da NAFDAC za su bukata a wurinsa matukar ya mika maganin don jiran amincewarsu.

"Kudin da za a bai wa NAFDAC kadai zai kai N600,000 ba tare da na gwajin ingancin ba wanda zai kai N1.5 miliyan.

"Toh gaskiya bayan da na ga yawan kudin, na ce bari in nemi taimako ta taron manema labarai. Ina da tabbacin cewa wannan maganin zai matukar taimakawa masu cutar korona," yace.

Mai maganin gargajiyar wanda ya musanta tsallake hukumar, ya yi bayanin cewa shirin an yi shi ne don samun wadanda za a hada guiwa da su tare da tallafi don hada kudin da za a dauka nauyin harhada maganin da rijistarsa.

COVID-19: Yadda NAFDAC ta tarwatsa taron kaddamar da maganin korona na gargajiya
COVID-19: Yadda NAFDAC ta tarwatsa taron kaddamar da maganin korona na gargajiya. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: UGC

KU KARANTA: Daga karshe: FG ta yi magana a kan bude makarantun gaba da sakandare

Ya yi bayanin cewa, ya samar da kadan na maganin don nunawa manema labarai ba wai da yawa ba don siyarwa.

Oni ya jaddada cewa maganinsa na iya kashe kwayar 'Virus' kuma babu shakka zai iya warkar da mai cutar korona.

Ya zarga cewa duk wani kokarin samun goyon baya daga ministan lafiya da sauran masu ruwa da tsaki ya gagara.

"Watakila da hakan ne jama'a za su kawo taimako. NAFDAC za su taimaka min tare da yin afuwa. Wannan ne dalilin yin taron manema labaran. Ban taba fitar da magani makamancin wannan don siyarwa ba. Ina da 'yan kwalabe kadan kuma zan nuna wa NAFDAC," yace.

Amma kuma jami'in cibiyar ya ce ba a tarwatsa taron don ba a aminta da maganin a kimiyyance ba.

Ya ce, "Wanda ya samar da maganin ya saba mu'amala da mu. Ya san yadda ake samun lambar ingancin daga NAFDAC don ya taba yi wa wasu magungunan sa har sau biyu.

"Amma kuma wannan maganin bai biyo ta hannun NAFDAC ba. A takaice, bai take dokar talla ba ta hanyar tallata maganin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel