Magu ya bayyana matakin da zai dauka saboda tsaresa da aka yi na kwanaki

Magu ya bayyana matakin da zai dauka saboda tsaresa da aka yi na kwanaki

- Dakataccen shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya yi barazanar fara yajin cin abinci a yayin da yake tsare

- Ana zargin Magu da handamar kudaden da aka samo daga mahandama kuma ya kwashe kusan mako daya a tsare

- Wasu majiyoyi sun ce akwai yuwuwar ba za a saki Magu ba har sai ya yi gamsasshen bayani game da zargin da ake masa

Wani rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa, dakataccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, zai fara yajin cin abinci.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Magu ya yanke wannan hukuncin ne bayan ganowa da yayi cewa fadar shugaban kasa za ta iya tsareshi har sai ya amsa laifukan da ake zargin sa da su.

Magu na fuskantar kwamitin fadar shugaban kasa na bincike bayan Antoni janar din tarayya, Abubakar Malami, ya bankado cewa ana sake kwashe kudin kasar nan da ake samowa.

Tuni, wasu 'yan siyasa da masu hannu da shuni a Najeriya da kasashen ketare, masu ikirarin cewa Magu da wasu jami'an EFCC sun damfaresu, suka fara mika kokensu a kan yadda aka kwace musu kudadensu ko kadarorinsu.

Magu ya bayyana matakin da zai dauka saboda tsaresa da aka yi na kwanaki
Magu ya bayyana matakin da zai dauka saboda tsaresa da aka yi na kwanaki. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Daga karshe: FG ta yi magana a kan bude makarantun gaba da sakandare

Magu tare da wasu hadimansa 7 sun shiga tasku bayan bayani ya kai ga fadar shugaban kasa a kan wasu harkokinsu.

Wata majiya daga fadar shugaban kasan, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce akwai yuwuwar a ci gaba da rike Magu har sai ya bada gamsassun amsoshi a kan zargin da ake masa.

Reno Omokri, tsohon hadimin fadar shugaban kasa ya wallafa a shafinsa na Twitter: "Kamar yadda salon tsare mutane da EFCC ke amfani da shi karkashin Magu, haka ake mishi amfani da shi.

"Magu zai tsareka sannan ya fara fitar da labarai na karya da gaskiya a kanka ga manema labarai. Abinda kwamitin ke yi mishi kenan."

Rahotanni sun kawo cewa an sake zargin dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahhim Magu, da kin bayar da cikakken bayani kan kadarori 332 da suka bata cikin 836 da aka kwato a watan Maris, 2018.

Wani rahoto daga kwamitin bayani a kan kudaden da aka samo (PCARA) ya bayyana cewa hukumar EFCC ta kasa bada bayanin wasu kadarorin biliyoyin naira.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai ya sanar, rahoton ya ce an samu asara da tagayyarar kadarori, motoci da sauran su duk da aka samo daga mahandama.

Ya kara da nuna damuwarsa kan yadda aka kasa adana dukiyoyin da gane darajarsu ta fuskacin tattalin arziki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel