'Yan sandan Dubai sun danƙa Hushpuppi a hannun Hukumar FBI ta Amurka

'Yan sandan Dubai sun danƙa Hushpuppi a hannun Hukumar FBI ta Amurka

Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, ta tasa keyar shahararren mutumin nan da ake zargi da damfara, Raymond Igbalode Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi, zuwa ga hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI.

Hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar 'yan sandan Dubai ta fitar a wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Alhamis.

Hukumar FBI ta yi mika godiya ta musamman da wanna namijin kokari da hukumar sa ido da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi na taka rawar gani wajen cafke Hushpuppi tare da mika mata shi.

A watan jiya na Yuni, rundunar 'yan sandan Dubai ta samu nasarar cafke Hushpuppi, Olalekan Jacob Ponle, wanda aka fi sani da Woodberry, da kuma wasu 'yan damfara a wani simame na musamman da ta yi wa lakabi da Fox Hunt.

'Yan sandan Dubai sun danƙa Hushpuppi a hannun Hukumar FBI ta Amurka
Hakkin mallakar hoto; Info Guide Africa
'Yan sandan Dubai sun danƙa Hushpuppi a hannun Hukumar FBI ta Amurka Hakkin mallakar hoto; Info Guide Africa
Asali: Instagram

Ababen zargin ana tuhumarsu da aikata munanan laifuka a UAE da suka hadar da halasta kudin haram da zamba ta yanar gizo, kutse da yin sojan gona wajen aikata laifuka daban-daban na satar kudin al'umma, inji 'yan sandan Dubai.

Kafin shigarsa hannu, Hushpuppi ya yi suna a kafofin sadarwa da dandalan sada zumunta saboda yadda yake wadaka da bayyana wa duniya irin arzikin da ya tara.

Daraktan hukumar binciken manyan laifuka na Dubai, Birgediya Jamal Salem Al Jallaf, ya ce "a simamen da ya yi sanadiyar shigar Hushpuppi hannu, an samu wasu takardu na shirin aikata wata gagarumar zamba ta kimanin dala miliyan 435."

KARANTA KUMA: Gwamnatin Oyo ta shata wa dalibai ka'idodin komawa makaranta

Ya ce "an kuma kwace fiye da dala miliyan 40.9 na tsabar kudi, motocin alfarma 13 wanda darajarsu ta kai kimanin dala miliyan 6.8, kwamfutoci 21, wayoyin salulu na zamani 47, da kuma adirishin fiye da mutum 1,926,400 da suka fada tarko."

Yayin ci gaba da bincike, an kuma gano wasu bayanan sirri na wasu mutane da kamfanoni daban-daban a kasashen ketare da suka hadar da asusun ajiya na bankuna da katunan ATM da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel