Gwamnatin Oyo ta shata wa dalibai ka'idodin komawa makaranta

Gwamnatin Oyo ta shata wa dalibai ka'idodin komawa makaranta

Gwamnatin jihar Oyo ta fitar da matakai daban-daban don dakile yaduwar Coronavirus a makarantu, yayin da daliban makarantun firamare da na sakandare a jihar ke shirin komawa makarantu a ranar 6 ga Yuli.

Kwamishinan ma'aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Mista Olasunkanmi Olaleye, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Ibadan a ranar Laraba.

Olaleye ya ce an ba da horo iri daban-daban ga shugabannin makarantu da malamai kan yadda za su saka idanu da mika rahoton duk wata alama ta rashin lafiya mai alaka da cutar COVID-19 ga hukumomin da suka dace.

Ya ce "gwamnatin jihar ta kafa cibiyoyin ko ta kwana a babban birnin jihar da kuma shiyoyi daban-daban tare da sanya wakili a kowace makaranta da za su rika ba da rahotanni na gaggawa kai tsaye ta hanyoyin sadarwa na musamman."

"Haka kuma an tanadi mai gadin kowane aji wanda za a dora wa nauyin aiki tare da wakilan da aka sanya a kowace makaranta wajen sanya idanun lura da gudanar da aikin ko ta kwana."

Gwamnan Oyo; Seyi Makinde
Hakkin mallakar hoto; Premium Times
Gwamnan Oyo; Seyi Makinde Hakkin mallakar hoto; Premium Times
Asali: Twitter

"Daga cikin sauran matakan da aka shata wanda dole sai an kiyaye sun hada da samar da wuraren wanke hannu a kowace mashiga ta makarantu."

"Haka kuma sai an tanadi sunadarin wanke hannu (sanitizer) a kofar kowane aji domin dalibai da malamai.su rika tsaftace hannayensu a duk lokacin da za su shiga."

"An kuma wajabta wa kowace makaranta da su tabbatar dalibai da malamansu sun kiyaye dokar bayar da tazara da sauran matakan dakile cutar korona da hukumar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC ta gindaya."

KARANTA KUMA: Asarar kudin haraji: Majalisa ta kira Ministar kudi, Emefiele, Magu da wasu kusoshin gwamnati

Kazalika, "ya ce an bukaci dalibai su rika zuwa makanta sanye da takunkumin rufe fuska tare da kiyaye sauran ka'idodi a yayin ba zai yi wa makarantu su dawwama a rufe ba," lamarin da ya ce hakan zai janyo mummunan koma baya ga harkar ilimi.

"Ina mai tabbatar muku da cewa matukar an kiyaye wannan matakai, muna da amincin cewa yara sai sun fi samun kariya a makaranta fiye da a gidajensu."

"Yace zaman galibin yaran a gida ya fi jefa su cikin hatsarin kamuwa da cutar korona saboda yadda wasun su ke rakiyar iyayensu zuwa kasuwanni ko kuma fita unguwa ko kuma aikensu zuwa wasu wuraren."

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, ana sa ran malamai za su koma makaranta a ranar 29 ga watan Yuni, yayin da dalibai za su koma a ranar Litinin 6 ga watan Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

`

Asali: Legit.ng

Online view pixel