Asarar kudin haraji: Majalisa ta kira Ministar kudi, Emefiele, Magu da wasu kusoshin gwamnati

Asarar kudin haraji: Majalisa ta kira Ministar kudi, Emefiele, Magu da wasu kusoshin gwamnati

Majalisar Dattawa ta gayyaci ministar kudi, kasafi da tsare-tsare; Zainab Ahmed, domin tayi bayani kan matakan dakile asarar kudaden shiga, da suka shafi rashin biyan haraji da sauran haramtattun ayyuka na hada-hadar kudi.

Majalisar yayin zamanta na ranar Laraba, ta gayyaci ministar da sauran kusoshin gwamnati masu rike da hukumomin hada-hadar kudi domin su bayyana a gaban kwamitinta na kudi da kuma na yaki da rashawa.

Kamar yadda jaridar Preimum Times ta ruwaito, majalisar ta yanke wannan shawara ne bayan kudirin da Sanata Gershom Bassey ya gabatar.

Sanata Bassey ya gabatar da wannan bukata ne domin a yi bita kan tsarin dakile haramtattun hanyoyin hada-hadar kudade tare da yi wa wadanda suka ki biyan haraji afuwa ta dawo da kudaden ba tare da an hukunta su ba.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare; Zainab Ahmed
Hakkin mallakar hoto; Nairametrics
Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare; Zainab Ahmed Hakkin mallakar hoto; Nairametrics
Asali: Twitter

A gabatarwar da ya yi, Mista Bassey ya ce Najeriya ta yi asarar akalla dala biliyan 140 ta haramtattun hanyoyin hada-hadar kudade a tsakanin shekarar 2000 zuwa 2014, musamman a harkar danyen man fetur.

Sauran kusoshin gwamnatin ta majalisar ta aikawa goron gayyata sun hadar da; gwamnan babban bankin Najeriya; Godwin Emefiele, shugaban hukumar tara haraji na kasa FIRS; Muhammad Mamman Nami.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya hana alfarma wurin daukan aiki a Najeriya - Lai Mohammed

Akwai kuma mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa EFCC; Ibrahim Magu, da Shugaban Hukumar da ke tattara bayanai a kan laifukan da suka shafi kudi da ta`addanci ta kasa NFIU; Modibbo Hamman-Tukur.

Sai kuma shugaban kamfanin man fetur a kasa NNPC; Mele Kolo Kyari, Shugaban Hukumar yakida cin hanci da rashawa a tsakanin ma'aikatan gwamnati ICPC; Bolaji Owasanoye da Manajan Darakta na Bankin NEXIM; Roberts U. Orya.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Majalisar wakilan tarayyar Najeriya za ta gudanar da bincike na musamman a game da yadda gwamnati ta ke ciyar da ‘yan makaranta kyauta a wasu makarantu da ke fadin kasar.

A ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, 2020, kwamitin da ke bibiyar asusun gwamnati ya bukaci gwamnatin tarayya da hukumar NBS ta yi mata bayani game da yadda ake ciyar da yara a makarantu.

Wannan kwamiti ya na zargin cewa akwai alamar tambaya game da alkaluman da gwamnati ta ke fitarwa na yaran da ake ba abinci kyauta a wasu makarantun firamare da ke kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel