Harkallar aiki 774,000: Sanata ya yi wa minsitan Buhari 'wankin babban bargo'

Harkallar aiki 774,000: Sanata ya yi wa minsitan Buhari 'wankin babban bargo'

Sanata Ifeanyi Ubah ya caccaki karamin ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo. Minsitan ya yi musayar yawu da 'yan majalisa a ranar Talatar da ta gabata.

Sanatan mai wakiltar mazabar Anambra ta kudu ya yi martani a kan rikicin da ya auku tsakanin Keyamo da 'yan majalisar tarayya a ranar Talata, 30 ga watan Yuni. Ya ce tun dama ministan ya je majalisar ne don nuna rashin da'a.

Ubah ya kara da cewa Keyamo ba shi bane ministan mai 'muhimmanci' ba.Ya ce; "Ina da damar yin magana a matsayina na dan kwamitin yada labarai na majalisar. Bai dace dan majalisar zartarwa yayi abinda ya yi ba.

"Aikin 'yan majalisa shine duba al'amura tare da duba ayyukan wadanda aka nada.

Harkallar aiki 774,000: Sanata ya yi wa minsitan Buhari 'wankin babban bargo'
Harkallar aiki 774,000: Sanata ya yi wa minsitan Buhari 'wankin babban bargo'
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda wani ya mayar da N1.8m da ya gani a kwalin taliya bayan siyayyar da yayi

"A matsayina na wakilin jama'ar mazaba ta, ba komai bane don na bukaci sanin yadda aka rarraba aikin yi ga 'yan Najeriya wanda dan majalisar zartarwa da aka nada ne ke jagoranta.

"A takaice ba shi bane ministan mai muhimmanci. A gaskiya rashin da'a zalla ya nuna.

"Ban san me sanata zai yi da aiki da za a biya N20,000 ko N30,000 ba wanda ya wuce tabbatar da an bai wa jama'ar mazabarsa. Idan aka bani ayyukan, za mu tabbatar da an raba su tsakanin jama'armu yadda ya dace don su muke wakilta.

"Amma bai wa mutanen da za su yi kwangilarsa tare da siyar da shi ko mika wa hannun wata cibiyar da za ta siyar bai dace ba ga 'yan majalisar tarayya.

"Na yi takaicin cewa bana majalisar a ranar Talata kuma ina magana ne a matsayin dan majalisa mai wakiltar Anambra ta kudu. Wannan rashin da'ar abun kushewa ne."

A ranar Talatar da ta gabata ne karamin minsitan kwadago da ayyukan, Festu Keyamo, ya yi musayar yawu da 'yan majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata a kan diban aiki karkashin NDE.

Rikicin ya fara ne a lokacin da darakta janar din NDE, Nasiru Ladan ya kasa kare kasafin kudinsu na N52 biliyan don daukar 'yan Najeriya 774,000 aiki karkashin NDE.

Ministan ya ce an bukaci ma'aikatarsa da ta kula da daukar aikin amma umarni ne daga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Lamarin da 'yan majalisar suka musanta tare da soma musayar kalamai da ministan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel