Ango ya rasu bayan shafawa sama da 'yan biki 100 cutar korona

Ango ya rasu bayan shafawa sama da 'yan biki 100 cutar korona

Wani biki a kasar India ya zama wurin raba cutar korona bayan da ango ya rasu sakamakon zazzabi mai zafi. Baya ga haka, ya shafa wa sama da 'yan bikin 100 tare da 'yan uwansa cutar korona.

Duk da shawarar da ya bai wa iyayensa na dage bikin, sun ki ji tare da ci gaba da shagalinsu.

Kamar yadda jaridar Hindustan Times ta bayyana, angon mai shekara 30 injinuya ne da ya fara zawo da zazzabi mai zafi tun kafin ranar 15 ga watan Yuni, amma 'yan uwansa sun tilasta shi da ya sha magani don su ci gaba da shagalinsu.

Bikin ya samu halartar sama da mutum 360 a Paliganj.

Sa'o'i 48 bayan nan, jikin ango ya rude kuma ya rasu a yayin da suke kan hanyar zuwa asibiti, kamar yadda jaridar ta sanar.

Tuni aka kai gawarsa ma'adanar gawawwaki ba tare da an yi masa gwajin cutar ba.

Bayan rasuwarsa, dukkan 'yan uwansa makusanta sun bayyana da cutar daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Yuni.

Ango ya rasu bayan shafawa sama da 'yan biki 100 cutar korona
Ango ya rasu bayan shafawa sama da 'yan biki 100 cutar korona. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda wani ya mayar da N1.8m da ya gani a kwalin taliya bayan siyayyar da yayi

Domin dakile yaduwar cutar, an samar da sansani inda aka killace dukkan 'yan bikin sannan aka yi ta diban samfur.

Daga cikin 'yan biki, mutum 86 sun tabbata dauke da cutar, Amma kuma amarya bata dauke da cutar.

"Duk da bashi da lafiya tun 14 ga watan Yuni kuma ya so a dage bikin, 'yan uwansa sun ki inda suka yi tunanin asarar da za su tafka sakamakon bikin da suka gama shiryawa," wani dan uwansa ya sanar da Hindustan Times.

Wani dan uwan angon wanda bai kamu da cutar ba, ya ce babu wanda yayi tsammanin cutar coronavirus ce ta kama angon.

"Saboda yankunan kauye duk babu cutar, hankalinmu kwance yake," dan uwan ya sanar.

"A ranar bikin, ya bayyana da zazzabi mai zafi, lamarin da yasa hankali ya tashi. Mun yi ta fatan ba cutar bace," dan uwan yace.

"Ya yi dukkan shirye-shiryen bikin bayan ya sha magani," cewar wani dan uwan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel