Yanzu-yanzu: Likitocin FMC Lokoja sun tafi yajin aiki

Yanzu-yanzu: Likitocin FMC Lokoja sun tafi yajin aiki

Likitocin cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi, sun fada yajin aiki wanda babu ranar komawa.

Bayan kammala wani taro da likitocin suka yi a ranar Laraba, sun yanke shawarar fadawa yajin aikin saboda barazanar da aka yi wa rayukansu.

Sun bayyana cewa "sun janye daga dukkan ayyuka" har zuwa lokacin da za a cika musu bukatunsu.

A wata takardar da suka fitar ta sanarwar yajin aikin, wanda suka tura wa jaridar The Cable, 'yan kungiyar 7 ne suka saka hannu.

Shugabannin kungiyar sun yi taron bayan sa'ao'i kadan da 'yan bindigar suka kai harin, sun yanke shawarar tafiya yajin aikin.

Wasu daga cikin wadanda suka saka hannu a takardar suna hada da Nnana Agwu, shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD); Samuel Obajemu, shugaban kungiyar hadin guiwa ta masana kiwon lafiya (JOHESU)

Akwai karin Abdulmalik Idris, shugaban kungiyar ma'aikatan jinya da ungozoma (NANNM) da John Omoche, shugaban kungiyar likitoci da ma'aikatab lafiya ta Najeriya (MHWUN).

Yanzu-yanzu: Likitocin FMC Lokoja sun tafi yajin aiki
Yanzu-yanzu: Likitocin FMC Lokoja sun tafi yajin aiki. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Ya'yan El-Rufai sun caccaki Atiku bayan dan sa ya yi wa El-Rufai habaici

'Yan bindiga a ranar Laraba sun kai hari Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, da ke Lokoja, Jihar Kogi inda suka tarwatsa taro a kan COVID-19 da ake gudanarwa.

Asibitin ta shirya yin taron manema labarai domin kira ga gwamnatin jihar ta samar da cibiyar yin gwajin COVID-19 a jihar kana ta tattauna kalubalen da ma'aikatan lafiya ke fuskanta a jihar saboda cutar.

The Cable ta ruwaito cewa yan bindigan sun isa asibitin cikin motoci guda uku inda suka fara harbe harbe da bindiga wadda hakan yasa mutane suka tarwatse.

Rahoton ya ce yan bindigan sun razana ma'aikatan lafiya inda suka kwace muhimman takardu da kwamfuta ta laptop daga hannunsu.

An kuma ce sun lalata wasu kayayyaki a asibitin. Kawo yanzu Rundunar Yan sandan jihar ba ta riga ta yi tsokaci a kan afkuwar lamarin ba.

A wani labari na daban, gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya musanta wanzuwar cutar korona. Ya ce an kawota don firgita jama'a da hana musu kwanciyar hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel