Annobar korona za ta kara tsananta talauci a tsakanin talakawa - Buhari

Annobar korona za ta kara tsananta talauci a tsakanin talakawa - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa dangane da yadda annobar cutar korona ta ke ci gaba da bazuwa a fadin duniya babu wani sassauci.

A yayin da likafar cutar ke ci gaba, shugaba Buhari ya ce tana kuma ci gaba da durkusar da tattalin arziki a fadin duniya.

Shugaban kasar yace babbar damuwarsa a halin yanzu ita ce yadda cutar ta ke ci gaba da yin mummunan tasiri na kara tsananta katutu na talauci a tsakanin mutanen da dama can sun yi tsamamo a cikinsa.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin babban mashawarci na musamman ga shugaban kasar kan harkokin sadarwa da hulda da al'umma, Mista Femi Adesina.

Mista Adesina ya ce shugaban kasar ya bayyana hakan a ranar Talata cikin wani sakon bidiyo da ya aikawa babban taron Majalisar Dinkin Duniya UN da aka gudanar kan dabarun kawar da talauci a duniya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Hakkin mallakar hoto; Reuters
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto; Reuters
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, an gudanar da taron ne a hedikwatar UN da ke birnin New York na Amurka, yayin kafa kungiyar yaki da fatara da talauci a duniya APE, shirin da Shugaban Majalisar, Farfesa Tijjani Muhammad-Bande ya assasa.

An samar da shirin APE ne domin ya zama wata hanya da mambobin Majalisar Dinkin Duniya, kasa da kasa da sauran masu ruwa da tsaki za su tallafa da matakan dakile talauci.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta fidda sunayen 'yan kwamitin da za su ja ragamar daukan matasa 774,000 a duk jihohin Najeriya

Buhari ya yi maraba da kafa wannan gagarumar kungiya, inda ya kara da cewa tuni dama Najeriya ta wuce kuma ta shige sahun gaba wajen yakar fatara da talauci, ta hanyar kafa shirye-shiryen inganta rayuwa.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin taron ne shugaba Buhari ya sanar da shirin da gwamnatinsa take yi na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci na da shekaru 10 masu zuwa.

Ya jaddada muhimmancin da gwamnatinsa ta bayar tare da mayar da hankalinta wajen shimfida dabarun bunƙasa tattalin arziki domin saukaka radadin talauci da al'umma ke fama musamman a wannan lokaci na annobar korona.

Kazalika, ya bayyana muhimmancin ilimi a matsayin wannan babban abin dogaro kuma mai dorewa wajen yakar fatara.

A halin yanzu akwai akalla ‘yan Najeriya miliyan 94 wadanda ke fama da kangin talauci kamar yadda kididdigar alkaluman Oxfam ta tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel