An birne bama-bamai a kananan hukumomi 7 na jihar Yobe (Sunaye) - 'Yan sanda

An birne bama-bamai a kananan hukumomi 7 na jihar Yobe (Sunaye) - 'Yan sanda

Akwai yuwuwar an birne wasu abubuwa masu fashewa a garuruwa 7 na jihar Yobe, jami'an 'yan sanda suka ce.

A wata takarda da ta fito daga kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim ya ce, "Rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta gano wasu abubuwa masu fashewa a kananan hukumomin Damaturu da Buni Yadi na jihar.

"Akwai yuwuwar an dasa abubuwa masu fashewa a garuruwan da suka hada da Geidam, Damaturu, Tadmuwa, Dapchi, Kanamma, Gulani da Buni Yadi.

"A yayin da damina ta tsaya, rundunar 'yan sandan na jan hankalin manoma da su kai rahoton duk wani abu da suka gani basu gane ba a gonakinsu.

"A misali, a ranar 20 ga watan Yunin 2020 a karamar hukumar Gujba, wani Adamu Haruna ya tsinta wani bam a gonarsa. A rashin sani ya kai shi gidansa.

"A yayin da yake kokarin budeshi, ya tashi inda ya raunata shi sosai. A halin yanzu yana asibiti inda yake jinya."

An birne bama-bamai a kananan hukumomi 7 na jihar Yobe (Sunaye) - 'Yan sanda
An birne bama-bamai a kananan hukumomi 7 na jihar Yobe (Sunaye) - 'Yan sanda. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

Jihar Yobe na daga cikin jihohin da mayakan Boko Haram suka yada zango a shekarun da suka gabata.

KU KARANTA: Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna)

A wani labari na daban, mutum tara suka rasa rayukansu sannan mutum shida sun samu miyagun raunika a kan rikicin gona da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a Malunje da ke kauyen Zadawa.

Kauyen na nan a yankin Hardawa da ke karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi. Jami'ai a karamar hukumar sun shiga rikicin wanda ya kai ga mutuwar wasu daga cikinsu a kauyen.

Gidan talabijin na Channels ya gano cewa, rikicin ya barke a ranar Litinin inda ya kai har safiyar Talata yayin da wasu fusatattun mutane suka dauka fansa.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ahmad Wakili, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce tuni aka tura jami'an tsaro yankin kuma komai ya daidaita tare da dawowar zaman lafiya.

Amma kuma wasu daga cikin wadanda suka samu rauni an mika su asibitin gwamnatin tarayya da ke Azare inda suke karbar taimakon likitoci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel