‘Yan sanda sun kashe ‘yan Najeriya 92 a cikin shekara guda kuma ana jinkirin bi musu haƙki

‘Yan sanda sun kashe ‘yan Najeriya 92 a cikin shekara guda kuma ana jinkirin bi musu haƙki

Bayan nazari kan rahotannin kafofin watsa labarai da bayanai daga Majalisar Harkokin Waje, Jaridar The Cable ta gano cewa 'yan sanda sun kashe akalla 'yan Najeriya 92 a cikin shekara guda da ta gabata.

Binciken da jaridar ta gudanar game da rahotanni daga kungiyoyi daban-daban da kuma mutanen da abin ya shafa, ya takaita ne daga tsakanin watan Maris na 2019 zuwa Fabrairun 2020.

Legit.ng ta fahimci cewa, binciken da aka gudanar bai tsawaita ba zuwa lokacin da aka shimfida dokar kulle sanadiyar annobar korona, inda a nan ma an yi ta kiraye-kiraye a kan take hakkin ɗan adam da jami'an tsaro ke yi.

Binciken bai tabo wadanda ake zargi da aikata laifi ba ko kuma wadanda suka mutu yayin da suke tsare a hannun jami'an sanda.

Haka kuma bai shafi wadanda sauran hukumomin tsaro suka kashe ba tare da hakki ba kamar hukuwar kwastam, inda aka ruwaito cewa a ranar 10 ga watan Maris na 2020, jami'anta sun kashe wasu mutane hudu a jihar Oyo.

Bayanai sun nuna cewa, wannan kisan gilla mai ban takaici da suka rika aukuwa akai-akai, an ruwaito cewa akasari sun faru ne yayin da mutane ke gudanar da zanga-zangar lumana ba tare da tunzura kowa ba.

Babban Sufeton 'Yan sanda na kasa; IGP Muhammad Adamu
Babban Sufeton 'Yan sanda na kasa; IGP Muhammad Adamu
Asali: Twitter

Wasu daga cikin manyan dalilan da aka ruwaito kan irin wannan kashe-kashe da 'yan sandan ke yi ba gaira babu dalili, sun hadar da kin bayar da cin hanci, jayayya da cacar baki, ko kuma fitar harsashi a bisa kure da kuma kokarin tarwatsa masu zanga-zanga.

"Misali, a ranar 13 ga Fabrairu, yayin da mazauna yankin Azagba a jihar Edo suka nuna rashin jin dadinsu game da mutuwar wani Frederick wanda wani dan sanda ya kashe suna tsaka da cacar baki, wata tawagar 'yan sanda da aka tura domin dakile zanga-zangar a karshe ta bige da kashe mutane hudu."

"Haka kuma, lokacin da mazaunan Sagamu a jihar Ogun suka yi dafifi don nuna rashin amincewarsu da mutuwar Tiamiyu Kazeem, kwararren dan wasan kwallon kafa na kungiyar Remo Stars wanda wani dan sanda ya kashe, a karshe jami'ai sun kashe uku daga cikinsu."

The Cable ta gano cewa galibin wannan rahotonni da aka samu sun ta'allaka ne da rundunar 'yan sanda ta musamman mai yaki da fashi da makami (SARS) a kasar, wacce ta yi kaurin suna wajen take hakkin dan adam.

KARANTA KUMA: An ƙirƙiri cutar korona saboda a haifar da tsoro da firgici a tsakanin mutane

Alal misali, a ranar 10 ga watan Agusta, yayin da jami'an rundunar SARS suke bin wani da ake zargi da laifi, a karshe sun harbi wata mata mai juna biyu wadda ta mutu nan take.

Rashin amincewa da ba da cin hanci ga jami’an ya haifar da mutuwar akalla mutane biyar, da suka hada da wani dan kabubu da aka ruwaito ya ki bayar da cin hancin Naira 100 ga ‘yan sanda.

Hakanan, wasu daga cikin kashe-kashen da aka ruwaito sun auku ne yayin artabu tsakanin 'yan sanda da mabiya kungiyar IMN ta Shi'a, tun gabanin yiwa kungiyar tozali a matsayin kungiyar ta'addanci.

Yayin da a lokuta mabanbanta 'yan sanda sun bayyana cewa mambobin IMN su kan ɓige da tayar da tarzoma yayin zanga-zangar su, kungiyar Amnesty International ta taba cewa jami'an tsaro ba sa bin doka wajen magance fushin kungiyar.

Wani abin mamaki shi ne yadda hatta jami’an ‘yan sanda kansu ba su tsira daga kisan gillar ba. An ruwaito cewa uku daga cikinsu sun kashe abokan aikin su a lokuta daban-daban ciki har da yayin tarwatsa masu zanga-zanga.

Da yawa daga cikin 'yan uwan wadanda abin ya shafa sun yi korafin cewa har yanzu ba a bi musu haƙƙin wadanda suka mutu ba. Sun ce ba a yi wa jami'an da abin ya shafa hukuncin da ya dace.

Ga jerin adadin mutanen da jami'an 'yan sanda suka kashe a tsakanin watan Maris na 2019 zuwa Fabrairun 2020:

Maris - 7

Afrilu - 5

Mayu - 2

Yuni - 1

Yuli - 19

Agusta - 6

Satumba - 19

Oktoba - 2

Nuwamba - 2

Dasumba - 7

Janairu - 7

Fabrairu - 15

Ga kuma jerin adadin mutanen da jami'an 'yan sanda suka kashe cikin jihohin Najeriya a tsakanin watan Maris na 2019 zuwa Fabrairun 2020:

Abia - 2

Akwa Ibom - 2

Anambra - 2

Bauchi - 6

Bayelsa - 3

Binuwe - 1

Delta - 1

Edo - 5

Ekiti - 2

Enugu - 1

Abuja - 19

Imo - 1

Kaduna - 5

Kano - 1

Katsina - 1

Ogun - 6

Ondo - 1

Oyo - 5

Filato - 1

Ribas - 3

Sakkwato - 3

Legas - 21

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel