Yadda wani ya mayar da N1.8m da ya gani a kwalin taliya bayan siyayyar da yayi

Yadda wani ya mayar da N1.8m da ya gani a kwalin taliya bayan siyayyar da yayi

'Yan Najeriya sun dinga cece-kuce tare da jinjinawa wani mutum mai suna Chidiebere Ogbonno, a kan yadda ya mayar da N1.8 miliyan da ya tsinta a kwalin taliyar da ya siya.

An gano cewa Ogbonna ya siya kwali daya tal na taliyar. Amma a lokacin da yake kan hanyar komawa gida, ya ji kwalin da nauyi ba kamar taliya ba.

Bayan yaga kwalin, ya ga kudi shake, lamarin da yasa ya juya tare da komawa shagon inda ya mayar musu da dukiyarsu.

An gano cewa, mai shagon ya adana cinikin da yayi ne a kwalin taliyar saboda gudun 'yan fashi da makami.

Kwalin ne aka mika wa Ogbonna bayan siyan kwalin taliyar.

Mutane da yawa sun jinjinawa Ogbonna a kan wannan kyakkyawan halin da ya nuna da nagarta.

Wasu kuwa ganinsa suke kamar wani bagidaje da wanda ba zai taba yin arziki ba, saboda wannan kudin da suka bayyana ya gudu.

Amma kuma, a matsayin kyautatawa ga gaskiyarsa, mai shagon ya dauka alkawarin bashi kwalin taliyar duk wata na tsawon watanni shida.

Yadda wani ya mayar da N1.8m da ya gani a kwalin taliya bayan siyayyar da yayi
Yadda wani ya mayar da N1.8m da ya gani a kwalin taliya bayan siyayyar da yayi. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna)

A wani labari na daban, wani mutum mai shekaru 42 mai suna Aliyu Adamu, wanda ya yi wa karamar yarinya fyade, ya sanar da rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa cewa mafarki yayi zai yi kudi.

Kamar yadda wanda ake zargin ya sanar bayan kama shi da aka yi a garin Lafia, ya ce mafarkinsa ya nuna masa cewa zai yi kudi idan ya yi wa karamar yarinya mai shekaru 5 zuwa 10 fyade.

Wanda ake zargin ya ce: "Ni dan asalin yankin Bukan Ari ne da ke karamar hukumar Lafia. Na yi mafarkin cewa idan na yi wa yarinya mai shekaru 5 zuwa 10 fyade zan zama hamshakin mai arziki.

"A saboda hakan ne na bi mafarkina domin cikar burina."

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe, ya kama wanda ake zargin tare da wasu mutum 44 masu laifukan da suka hada da fyade, fashi da makami da kungiyar asiri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng