An ƙirƙiri cutar korona saboda a haifar da tsoro da firgici a tsakanin mutane

An ƙirƙiri cutar korona saboda a haifar da tsoro da firgici a tsakanin mutane

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi zargin cewa, ƙirƙirar cutar korona aka yi saboda kawai a haifar da tsoro da firgici a tsakanin mutane.

Furucin gwamnan ya zo ne a yayin da yake kara jaddada cewa, ba cutar korona ce ta yi sanadiyar mutuwar babban alkalin jiharsa ba, Mai Shari'a Nasir Ajana.

Gwamna Bello ya bayyana hakan ne a yayin zaman addu'ar sadakar uku na makokin marigayi Ajana da aka gudanar a ranar Talata.

Mai shari'a Ajana ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti cikin birnin Abuja.

Ya bayyana cutar korona a matsayin annoba mafi muni fiye da ta'addancin fashi da makami da na Boko Haram, yana mai bayyana takaicin cewa ƙirƙirarta kawai akayi domin a yaudari 'yan Najeriya.

Gwamnan jihar Kogi; Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi; Yahaya Bello
Asali: Facebook

Ya shawarci 'yan Najeriya a kan kada su fada cikin tsoro ko wani sharri kan batun cutar korona, ya na mai cewa, "cuta ce da aka shigo da ita, ana yada ta da muzgunawa mutane ba gaira babu dalili".

Ya yi nuni da cewa babu abin da ke saurin kashe mutane fiye da tsoro da firgici, yana mai kira ga mutane a kan kada su yarda cutar ta yi mummunan tasiri a kansu.

A yayin da ya ke jaddada cewa an halicci ƙwayoyin cutar korona ne kawai domin haifar da tsoro, a tsakanin mutane, ya koka da yadda aka ƙirƙiri cutar don a takaice rayuwar mutane.

Ya ce "ko kwararrun kiwon lafiya da masana kimiya su yarda ko kar su yarda, an bullo da cutar covid-19 ne domin a gajarce tsawon rayuwar mutane."

"Cuta ce da ake bazata a Najeriya ta karfin tsiya."

KARANTA KUMA: Tattalin arziki: Buhari ya jagoranci wani zama na musamman a fadar shugaban kasa

Gwamnan ya bayyana marigayi Ajana a matsayin kwararren masanin shari'a mai matukar kaunar zaman lafiya.

A yayin gabatar da hudubarsa, Mai Shari'a Nuruddeen Khalifa, ya kirayi 'yan Najeriya da su yi kwaikwayon kyawawan dabi'u na marigayi Ajana tare da horo a kan yin rayuwa mai kyawu da za a yi koyi da ita.

A nasa jawabin, dan marigayin Ajana, ya yi godiya ga gwamnatin jihar bisa goyon bayan da ta bai wa mahaifinsa, yana mai bayyana wannan rashi da suka yi a matsayin mai raɗaɗin gaske.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel