Ka zo ka ziyarce mu a birnin Fatakwal - Wike ya roki shugaba Buhari

Ka zo ka ziyarce mu a birnin Fatakwal - Wike ya roki shugaba Buhari

- Gwamna Wike ya bukaci Shugaba Buhari da ya ziyarci jiharsa ta Ribas

- Gwamnan ya jinjinawa shugaba Buhari da ya amince da maido da kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 78.9 zuwa asusun gwamnatin jiharsa

- Wike ya ce a yanzu jiharsa a shirye ta ke ta hada kai da gwamnatin tarayya

Gwamna Nyesom Wike, ya yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amincewarsa ta maido da kudaden da yawansu ya kai naira biliyan 78.9 zuwa asusun gwamnatin jihar Ribas.

Shugaba Buhari ya amince da fitar da kudaden ne sakamakon wasu muhimman ayyuka na gine-ginen manyan tituna mallakar gwamnatin tarayya da gwamnati jihar Ribas ta aiwatar.

Wike ya bayyana hakan ne cikin wani sako na yabo da godiya ga shugaban kasa da ya wallafa a kan shafinsa na dandalin sada zumunta.

Gwamnan jihar Ribas; Nyesom Wike
Hakkin mallakar hoto; Fadar Gwamnatin jihar Ribas
Gwamnan jihar Ribas; Nyesom Wike Hakkin mallakar hoto; Fadar Gwamnatin jihar Ribas
Asali: Facebook

KARANTA KUMA: An yi jana'izar Dattijon da motocin kwamandan sojin kasa suka kashe a Katsina

Gwamnan ya kuma kwarara yabo da jinjina a kan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a bisa goyon bayan da ya ke yiwa jiharsa.

"Ina so na yi amfani da wannan dama na gayyaci shugaban kasa da ya kawo wa jiharmu ziyara domin ya ganewa idanunsa ayyukan da muka gudanar da kudaden domin ci gaban jihar da kuma al'umma."

Haka kuma Legit.ng ta ruwaito cewa, Yariman kasar Saudiyya, Muhammad Bin Salman, ya yi hira da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da takwaransa na kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa.

Yayin tattaunawarsu, shugabannin sun yi magana a kan kara kulla zumunci da juna da kuma sauran wasu batutuwa da suka shafi bukatun kasashensu da tallafin da zasu iya bawa juna wajen cimma manufofinsu.

Yarima Salman da Buhari sun kara tattaunawa a kan daidaita farashin man fetur a kasuwar duniya a matsayinsu na shugabannin kasashen da ke zaman mambobi a kungiyar kasashe ma su arzikin man fetur (OPEC).

Kazalika shugabannin sun kara tattaunawa a kan hanyoyin sake inganta kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel