An yi jana'izar Dattijon da motocin kwamandan sojin kasa suka kashe a Katsina

An yi jana'izar Dattijon da motocin kwamandan sojin kasa suka kashe a Katsina

An yi jana'izar dattijon da ya rasa ransa a wani hatsarin mota da ya danganci ayarin motocin wani Kwamandan sojin kasa na Najeriya, Birgediya Janar Warrah Idris.

Hatsarin ya auku ne a ranar Litinin cikin jihar Katsina, yayin da ayarin motocin kwamandan sojin suka buge dattijon yana haye a kan baburinsa.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Alhaji Salisu Ibrahim, ya yi gamo da ajali ne bayan da ayarin motocin ke hanyarsu ta dawowa wajen daukan babban sojan bayan sun tsaya shan mai.

Mashaida wannan mummunan lamari sun bayyana cewa hatsarin ya auku ne a daura a kwanar gidan Mani da ke kwaryar birnin Katsina.

An tattaro cewa, dattijon mai shekaru 75 nan take ya mutu.

Jana'izar Alhaji Salisu Ibrahim
Hakkin mallakar hoto; Sahara Reporters
Jana'izar Alhaji Salisu Ibrahim Hakkin mallakar hoto; Sahara Reporters
Asali: Twitter

Mukaddashin kakakin rundunar sojin kasa na Najeriya, Kanal Sagir Musa, ya tabbatar da wannan lamari cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce tawagar dakarun sojin wanda Birgediya Janar Idris ya jagoranta, ta ziyarci iyalan marigayi Salisu Ibrahim domin jajanta musu.

Sa dai a rahoton da jaridar Sahara Reporters ta ruwaito, ya bayyana cewa, ayarin motocin Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ne suka buge dattijon.

KARANTA KUMA: Mutuwar Osinowa: Majalisar Dattawa ta ɗage zamanta na ranar Talata

Haka kuma Jaridar Aminiya ta ce dattijon mai inkiyar 'Yar Yara ya rasa ransa ne a yayin da ya ke kan hanyarsa ta kai katin gayyatar daurin auren diyarsa da za a yi ranar Juma'a mai zuwa.

Kamar yadda jaridar ta ruwaito, "wani ganau ya ce ya ga lokacin da ayarin motocin sojin da ke gudu suka buge tsohon a kan layin Yahaya Madaki da ke cikin birnin Katsina."

"Salisu Ibrahim ya rasa ransa ne sadda ya zo ketare hanya a kusa da Gidan Mani inda motocin suka dake shi kuma nan take ya riga mu gidan gaskiya."

"Motar da ke cikin ayarin da ta bige dattijon dai ba ta tsaya ba ko kuma direban ya nuna nadamar abin da ya faru", inji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel