Mutuwar Osinowa: Majalisar Dattawa ta ɗage zamanta na ranar Talata

Mutuwar Osinowa: Majalisar Dattawa ta ɗage zamanta na ranar Talata

Majalisar dattawa ta ɗage zamanta na ranar Talata tare da yin shiru na minti daya domin yin jimamin mutuwar Sanata Bayo Osinowo mai wakiltar shiyyar Legas ta Gabas.

Ajali ya katse hanzarin dan majalisar mai shekaru 64 a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, biyo bayan wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, wanda ya jagoranci zaman majalisar na ranar Talata a takaice, ya ɗage zamanta zuwa ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, kamar yadda aka saba a al'adar majalisar.

Jigo cikin dattawan majalisar, Yahaya Abdullahi, shi ne ya gabatar da kudirin ɗage zaman majalisar kuma aka aminta da shi cikin hazari babu ko jayayya.

Sanata Bayo Osinowo
Sanata Bayo Osinowo
Asali: Twitter

Haka zalika, shugaban 'yan tsiraru watau marasa rinjaye na majalisar, Enyinnaya Abaraibe, shi ne ya yi gaggawar goyon bayan kudirin ɗage zaman majalisar da Sanata Abdullahi ya gabatar.

Sanata Osinowo ya mutu kwanaki hudu bayan dawowa daga hutun makonni biyu da majalisar dokoki ta tarayya ta yi a ranar 11 ga watan Yuni.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Sanatan ya mutu ne a babban asibitin First Cardiologist dake Legas.

Bayan zaman majalisar da aka gudanar a yau Talata, an kuma bude rajistar shigar da sakonnin gaisuwa da ta'aziyar mutuwar Sanata Osinowa a daidai mashigar zauren majalisar, inda sanatoci suka yi tururuwa wajen rattaba hannu.

Marigayi Osinowa shi ne jerin Sanata na hudu da mai yankan kauna ta katsewa hanzari a sabuwar majalisa ta 9 a tarihin kasar tun kafuwarta a shekarar da ta gabata kawo yanzu.

KARANTA KUMA: Babu wani lokaci da na yi furucin ɗan ƙabilar Ibo ba zai taɓa zama shugaban kasar Najeriya ba - Shettima

Sauran 'yan majalisar dattawan uku da suka riga mu gidan gaskiya a bana sun hadar da Sanata Benjamin Uwajumogu, Sanata Ignatius Longjan, da kuma Sanata Rose Oko.

Mataimakin shugaban majalisar ya yi kira da a yiwa sanatocin da suka riga mu gidan gaskiya addu'a.

Shugaban kwamitin harkokin sadarwa da hulda da al'umma na majalisar, Sanata Ajibola Basiru, ya misalta marigayi Osinowo a matsayin amintacce kuma na hannun daman tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu.

A sanarwar da Sanata Basiru ya fitar, ya ce marigayi Osinowo mutum ne mai kirki kuma mai kishin kasa wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaban siyasa a jiharsa ta Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel