Harkallar diban aiki: 'Yan majalisa sun kori ministan Buhari bayan musayar yawu

Harkallar diban aiki: 'Yan majalisa sun kori ministan Buhari bayan musayar yawu

Karamin minsitan kwadago da ayyukan, Festu Keyamo, ya yi musayar yawu da 'yan majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata a kan diban aiki karkashin NDE.

Rikicin ya fara ne a lokacin da darakta janar din NDE, Nasiru Ladan ya kasa kare kasafin kudinsu na N52 biliyan don daukar 'yan Najeriya 774,000 aiki karkashin NDE.

Ministan ya ce an bukaci ma'aikatarsa da ta kula da daukar aikin amma umarni ne daga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Lamarin da 'yan majalisar suka musanta tare da soma musayar kalamai da ministan.

Harkallar diban aiki: 'Yan majalisa sun kori ministan Buhari bayan musayar yawu
Harkallar diban aiki: 'Yan majalisa sun kori ministan Buhari bayan musayar yawu. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Buratai ya koma Katsina, garinsu shugaba Buhari

Karamin minsitan kwadago da ayyuka, Festus Keyamo ya yi musayar yawu da 'yan majalisar dattawa a kan shirin diban ma'aikata 774,000 da gwamnatin tarayya za ta yi.

A watan Afirilun 2020, Zainab Ahmed, ministan kudi, kasafi da tsarin kasa, ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amiince da dibar 'yan Najeriya 774,000 aiki.

Wadanda za a diban za a saka su ayyuka na musamman ne a karkashin hukumar diban aiki (NDE).

A ranar Talata, Keyamo ya bayyana gaban kwamitin hadin guiwa na majalisar dattawa da wakilai tare da darakta janar na NDE.

An bukacin darakta janar na NDE, Ladan da ya yi bayanin yadda ya kafa kwamitin mutum 20 don fara aikin amma sai yace kwamitin mutum takwas kacal ya sani.

'Yan majalisar sun juya kan Keyamo inda suka fara tambayarsa tare da zarginsa da kwace shirin daga NDE.

A wannan lokacin, rikici ya barke tsakanin Keyamo da wasu 'yan majalisar inda suka dinga ihu da hargagi ga juna.

'Yan majalisar sun bukaci a kebance don yin tattaunawar amma Keyamo ya ce bai aminta da hakan ba.

A yayin da yake ihu, Keyamo ya ce: "Ta yaya za ku bayyana rashawa a rufe babu shaidu? Ta yaya za ku bayyanata? Sai na yi martani a kan abinda yace. Ba za ku yi magana sannan ku yi tsammanin in yi shiru ba."

A take wasu daga cikin 'yan majalisar suka zuba ihu a saman muryoyinsu inda suka ce: "Fice daga nan. Bace mana da gani. Ina sajan yake?"

A take aka umarcesa da ya fita daga dakin sauraron.

A yayin zantawa da manema labari, Keyamo ya zarga 'yan majalisar da yunkurin kwace shirin wanda yake karkashin ma'aikatarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel