Babu wani lokaci da na yi furucin ɗan ƙabilar Ibo ba zai taɓa zama shugaban kasar Najeriya ba - Shettima

Babu wani lokaci da na yi furucin ɗan ƙabilar Ibo ba zai taɓa zama shugaban kasar Najeriya ba - Shettima

Shugaban kungiyar tuntuba ta Matasan Arewa, Alhaji Shettima Yerima, ya karyata wata sanarwa da ake danganta sa da ita ta nuna kiyayya ga ‘yan kabilar Ibo.

Alhaji Yerima ya musanta zargin da ake masa na cewa 'yan kabilar Ibo daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ba za su taba samun shugabancin kasar ba.

Idan ba a manta ba a makon jiya ne tsohon gwamnan tsohuwar jihar Anambra a jamhuriya ta biyu, Dr. Jim Nwodo, ya ce kujerar shugaban kasa a 2023 ba ta kowa ba ce sai 'yan kabilar Ibo.

Biyo bayan wannan furuci na Sanata Nwodo, dandalan sada zumunta suka rikide da rahotannin cewa ba za a taba bai wa 'yan kabilar Ibo damar mulkar kasar nan ba.

Shugaban kungiyar tuntuba ta Matasan Arewa, Alhaji Shettima Yerima
Shugaban kungiyar tuntuba ta Matasan Arewa, Alhaji Shettima Yerima
Asali: Twitter

Sai dai a yayin ganawa da manema labarai a jiya Litinin, Yerima ya ce tabbas wannan rahotanni sun samo asali ne daga masu neman kada a zauna lafiya da babu abinda suka sa gaba sai aniyar rarraba kan al'umma.

Ya ce abin da kadai Najeriya ke bukata a wannan lokacin shi ne cancanta wanda ya yi imanin cewa mutanen kudu maso gabas su na da ita domin ciyar da kasar gaba.

Da wannan ne Alhaji Yerima ya nesanta kansa daga rahotannin, yana mai jaddada cewa galibin makusantansa da abokan hulda sun fito ne daga yankin na Kudu maso Gabas.

"Ni dan Najeriya ne na hakika kuma na yarda da cewa kowane dan kasa yana da cikakken 'yanci musamman a kasa irin tamu."

KARANTA KUMA: Motocin babban kwamandan soji sun buge dattijo a Katsina har lahira

"Ba zan iya tuna lokacin da na yi wannan furuci da ake danganta ni da shi a yanzu ba, amma ban san manufar da makiyan kasar nan ke son su cimma ba."

"Gaskiyar magana ita ce, labarin da ake jingina min shi ba gaskiya bane illa iyaka kage da kuma shaci fadi."

"Sai dai babu shakka wannan lamari a bayyane ya ke, domin kuwa akwai wasu mutanen da ke da burin wargaza kasar nan kuma babu abin da suke fata face ganin an samu rarrabuwar kai a tsakanin al'umma."

"Kada a manta, matar da na aura ta fito ne daga yankin Kudancin Najeriya. Saboda haka ta ya kuma kulla kiyayya a tsakanin 'yan uwana 'yan Najeriya," inji Yerima.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel