Shugaba Buhari ya rage tsadar kudin aure a wuraren bauta - Minista

Shugaba Buhari ya rage tsadar kudin aure a wuraren bauta - Minista

Gwamnatin Tarayya ta zaftare kuɗaɗen da ake caji wajen gudanar da ayyukan da suka shafi daurin aure na doka a fadin ƙasar.

Gwamnatin ta amince da sake yin nazari game da kuɗaɗen da ake biya wajen mallakar takardun shaidar aure karkashin Dokar Aure ta CAP M6 LFN 2004 da za ta aiki fara daga ranar Laraba, 1 ga Yuli.

Mista Mohammed Manga, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, babban birnin kasa.

Manga ya ce Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ta hannun Babbar Sakatare kuma Babbar magatakarda ta Aure a Najeriya, Georgina Ehuriah.

Aregbesola ya ce an yi wannan sauyi ne bayan shawarwarin da masu ruwa da tsaki suka gabatar a tarukan wayar da kai da aka gudanar a duk fadin kasar a shekarar 2019.

Ministan Harkokin Cikin Gida; Rauf Aregbesola
Hakkin mallakar hoto; @raufaregbesola
Ministan Harkokin Cikin Gida; Rauf Aregbesola Hakkin mallakar hoto; @raufaregbesola
Asali: Twitter

A cewarsa, an rage kudaden da ake caji na bayar da takardar shaidar sabon Aure a wuraren bauta daga N30,000 na shekaru biyu zuwa N6,000 da za a biya a kowace shekara. Ana iya biyan na shekara biyar karon farko.

Domin kuma sabunta lasisin aure a wuraren bauta, an yarda a biya N5,000 a kowace shekara, na tsawon shekaru uku, sabanin yadda a baya ake biyan N30,000 duk shekara, in ji shi.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Matakai 8 da gwamnatin tarayya ta sake dauka na sassauta dokar kulle

Hakanan an rage kudin aure daga N21,000 zuwa N15,000 yayin da aka rage lasisin kudin aure na musamman daga N35,000 zuwa N25,000.

A wani rahoto na daban da Legit.ng ta ruwaito, Masana kimiyya sun kara bankado wata cuta sabuwa mai kamanceceniya da mura a China wacce suka ce akwai yuwuwar ta zama annobar duniya.

Cutar ta bayyana ne a kwanan nan kuma an gano tana tattare ne da aladu. Amma kuma masanan sun tabbatar da cewa mutane za su iya kamuwa.

Masanan sun damu da cewa akwai yuwuwar cutar ta rikide ta yadda za ta ci gaba da yaduwa daga mutum zuwa mutum har ta haddasa annoba a fadin duniya.

Duk da yake, ba wata babbar matsala bace ta gaggawa, amma sun tabbatar da cewa akwai dukkan alamun da ke nuna cewa cutar za ta iya sauyawa don shafar mutane, lamarin da yasa ake bukatar bibiyarta.

Sun ce sabuwar cuta ce kuma ba dole garkuwar jikin dan Adam ta iya karesu daga ita ba.

Masanan sun wallafa a mujallar Proceedings of National Academy of Sciences cewa ya dace a hanzarta bullo da matakai tsaurara na dakile yaduwar cutar a jikin aladu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel