Allah ya yi wa wani hamshakin dan kasuwar Najeriya rasuwa

Allah ya yi wa wani hamshakin dan kasuwar Najeriya rasuwa

Wani hamshakin dan kasuwa kuma mai taimakon al'umma, Bode Akindele, ya rasu. An gano cewa shugaban Madandola Groups ya rasu a ranar Litinin a garin Legas bayan cikarsa shekaru 88.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya kwatanta mutuwar tsohon dan kasuwar Ibadan din da babban rashi ga jihar Oyo tare da Najeriya baki daya.

A wata takarda da Makinde ya bai wa manema labarai ta hannun sakataren yada labaransa, Taiwo Adisa, ya ce "Labarin mutuwar jigo a jiharmu, Bode Akindele ya rikemu a matsayin babban abun firgici.

"Zan iya tunawa da cewa, a kwanaki kadan da suka gabata ne jihar Oyo ta bukaci tallafi a kan annobar korona, Baba Akindele na daya daga cikin wadanda suka bada tallafin har N25 miliyan.

“Abun jimami ne da alhini yadda muka rasa shi a wannan lokacin.. Ina fatan Ubangiji ya bai wa dukkan iyalansa da jama'ar jihar hakurin jure rashinsa."

A yayin martani a kan mutuwar Parakoyi na kasar Ibadan, Olubadan, Sarki Saliu Adetunji, ya ce ya shiga matukar dimuwa da wannan mutuwar da ta zo bayan kwanaki hudu tak da rasuwar tsohon gwamna Abiola Ajimobi.

Olubadan ya ce, "Duk da ya rayu na tsawon shekaru 82, za mu iya cewa ya tsufa, amma za mu yi jimamin rashinsa ne saboda gurbin da ya bari wanda da kyar a iya cike shi."

Parakoyi na Ibadan shine wanda ya kirkiri gidauniyar Bode Akindele. Akindele sanannen mai taimakon jama'a ne wanda ya kwashe shekaru yana aikin taimako.

Babban dan kasuwar ya bada tallafin miliyoyin naira ga gwamnatocin tarayya da na jihar don yakar annobar korona a fadin kasar nan.

Allah ya yi wa wani hamshakin dan kasuwar Najeriya rasuwa
Allah ya yi wa wani hamshakin dan kasuwar Najeriya rasuwa. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: FG ta amince da bude makarantu, ta yanke karin hukunci 2

A cikin shekaru da dama da suka wuce, ya saba daukar nauyin karatun dalibai a mataki daban-daban na karatu.

Kungiyar matasa ta Bode Akindele tana hada guiwa da jami'ar jihar Ibadan wurin koyar da dalibai sana'o'in dogaro da kai don amfaninsu ko bayan kammala karatu.

Mahaifiyarsa mai suna Rabiatu Adedigba, hamshakiyar mai arziki ce da ke kasuwanci tare da siyasa.

Akindele ya halarci makarantar Olubi Memorial School da ke Ibadan tare da Lisabi Commercial College da ke Abeokuta. Wannan horarwar da ya samu ce ta bashi damar zama babban dan kasuwa.

Bayan kammala sakandarensa, Akindele ya so tafiya Ingila karatun shari'a amma al'amuran kasuwancinsa ya hana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel