Jihohi 10 da suka fi kowanne yawan mutane masu cutar korona a Najeriya
Duk da fadi-tashin da mahukuntan lafiya ke ci gaba da yi babu dare babu rana, cutar korona na ci gaba da bazuwa tamkar wutar daji a Najeriya da sauran sassa na duniya.
A halin yanzu dai, alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC sun tabbatar da cewa, cutar korona ta harbi mutum 24,567 cikin duk jihohin da ta bulla a kasar.
Sai dai yadda cutar ta ke yaduwa a kasar ya sha ban-ban a tsakanin jihohin da ta bulla.
A yayin da wasu jihohin na da tulin mutane da cutar ta harba, wasu kuwa mutane 'yan kalilan ne suka kamu da ita a cikinsu.

Asali: Twitter
Har ila yau dai jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, sai da masu ruwa da tsaki sun ce rashin kayan aiki da karancin ma'aikatan lafiya ya yi tasiri a kan lamarin.
KARANTA KUMA: Afrika ta Kudu da kasashen Afrika 16 da suka fi kamuwa da cutar korona
Kididdigar alkaluman da NCDC ta fitar a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni, ta nuna cewa akwai mutum 14,995 da har yanzu su na dauke da kwayoyin cutar a fadin kasar nan.
Taskar bayanai ta hukumar ta sanar da cewa, an sallami mutum 9,007 daga cibiyoyin killace masu cutar da ke fadin kasar yayin da tuni mutum 565 suka riga mu gidan gaskiya.
Ga jerin jihohi 10 da mutane suka fi kamuwa da cutar a Najeriya:
1. Lagos - 10,144
2. Abuja - 1,792
3. Oyo - 1,306
4. Kano - 1,200
5. Rivers - 1,056
6. Edo - 962
7. Delta - 912
8. Ogun - 782
9. Kaduna - 703
10. Katsina - 549
Ga jerin jihohi 10 da mutane suka fi mutuwa sakamakon cutar a Najeriya:
1. Lagos - 126
2. Kano - 51
3. Ribas - 38
4. Edo - 35
5. Abuja - 32
6. Borno - 32
7. Delta - 22
8. Katsina - 22
9. Ondo - 19
10. Ogun - 18
Ga jerin jihohin da aka fi samun yawan mutanen da suka warle daga cutar:
1. Lagos - 1,592
2. Kano - 866
3. Ribas - 584
4. Abuja - 558
5. Ogun - 539
6. Oyo - 506
7. Bauchi - 439
8. Kaduna - 449
9. Borno - 418
10. Gombe - 346.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng